Hukumomi a Georgia sun cafke tsohon shugaban kasar Mikheil Saakashvili ranar Juma’a jim kadan bayan dawowarsa daga gudun hijira, bayan da sukayi fito na fito da magoya bayansa a cikin ‘yan adawa.
Saakashvili, fitaccen mai fafutukar neman canji na Yammacin Turai wanda ya bar ƙasar ta Georgia a karshen wa’adin mulkin shugabancin sa na biyu a shekarar 2013, ya ba da sanarwar dawowar gida a wani saƙon bidiyo.
Abokan hamayyarsa a jam’iyyar Dream Party ta Georgia sun yi gargadin cewa za a kama shi kan zargin cin zarafin ofishinsa muddun ya koma gida, kuma Firanminista Irakli Garibashvili ya ce an hanzarta tsare shi.
A wani labarin nadaban shugaban hukumar da ke sa ido kan makamashin nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa, an cimma matsaya ta wucin-gadi” na tsawon watanni uku da zai baiwa hukumar damar ci gaba da sanya ido kan Iran, duk da cewa matakin sahalewar zai takaita daga ranar Talata.
Shugaban Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya ta Duniya da ke Vienna, Rafael Grossi wanda ya shaida hakan ga manema labarai, bayan tattaunawa da shugabannin Iran, yace, matakin nada matukar tasiri wajen dinke barakar da ake da shi yanzu haka.
Grossi ya bayyana ci gaban ne, bayan shafe kwanaki biyu yana ziyara a Iran, inda ya tattauna da shugabannin Iran kan shirinta na nukiliya, sa’o’i gabannin cikar wa’adin da ta diba na takaitawa hukumar, gudanar da bincike, ciki harda ministan harkokin wajen kasar Mohammad Javad Zarif, da kuma shugaban hukumar sarrafa makamashi na kasar Ali Akbar Salehi.
Tun a watan Disamba ne, Majalisar dokokin Iran wacce ke da rinjayen masu ra’ayin rikau ta zartar da doka inda ta bukaci kasar ta dakatar da masu binciken hukumar idan har Amurka ta gaza cire mata takunkuman da ta kakaba mata, dokar za ta fara aiki daga gobe Talata.
Grossi baiyi cikakken bayani game da ayyukan da hukumar ta IAEA, ba za ta iya yi ba, amma ya tabbatar da cewa ba za a rage yawan jami’an da ke cikin kasar ta Iran ba, kuma za a ci gaba da binciken gaggawa a karkashin tsarin na wucin gadi.
Matakin da ke zuwa yayin da Amurka da Tarayyar Turai suka kara azama a kokarinsu na ceto yarjejeniyar nukiliyar 2015, wacce ke daf da rugujewa tun bayan da tsohon shugaba Donald Trump ya janye Amurka daga cikinta.
Muddin wa’adin ya cika ba tare da Amurka ta janye takunkuman ba, Iran na da damar hana masu sa idon na hukumar kula da makamashin nukiliyar domin hakan na cikin hakkokin ta.