Geng Shuang, mataimakin wakilin kasar Sin a MDD, ya halarci taron kwamitin sulhu dangane da batutuwan mata, da zaman lafiya, gami da tsaro, a jiya Laraba, inda a madadin gwamnatin Sin ya yi kira ga kasashen duniya da su gaggauta warware rikici ta hanyar siyasa, don magance cin zarafin mata, da tabbatar da tsaronsu, tare da samar musu wani yanayi na kwanciyar hankali, don ci gaban mata.
Jami’in Sin ya kara da cewa, ya kamata a ba ’yan mata damar raya kansu, don tabbatar da daidaito tsakanin maza da mata, da samun ci gaban tattalin arzikin duniya mai dorewa.
A cewarsa, ci gaban tattalin arziki shi ne tushen warware matsaloli daban daban, wanda zai tabbatar da daga matsayin ’yan mata. Saboda haka, dole ne kwamitin sulhun MDD da gamayyar kasa da kasa, su aiwatar da tunanin raya tattalin arziki don tabbatar da zaman lafiya, da baiwa ’yan mata damammaki na raya kansu, da samun karin kwarewar aiki.
Ban da haka, jami’in ya ce kasar Sin har kullum tana kokarin yayata ra’ayin samun daidaito tsakanin maza da mata, da goyon bayan ajandar MDD ta mata, da zaman lafiya, da tsaro.
Kasar na son karfafa hadin gwiwa tare da bangarori daban daban, da kara ba da gudummawa don tabbatar da samun ci gaba da nasarorin a fannin harkokin mata a duniya. (Bello Wang)
Source LEADERSHIPHAUSA