A martanin farko da ya mayar bayan da ‘yan Taliban suka kwace iko da Kabul, shugaba Ra’isi, ya ce ya kamata gazawar amurka da ficewar sojojin ta, ya zama wata dama ta tabbatar da zaman lafiya da tsaro a Aghanistan.
Ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin Afghanistan dasu cimma matsaya ta siyasa domin jagorancin kasar.
Iran, ta kuma ce a shirye ta ke ta taimaka wajen dawo da zaman lafiya a makobciyar kasar Afghanistan.
Dama dai Iran ta jima da take kalubalantar kasancewar sojojin Amurka a kasar ta Afghanistan dama yankin baki daya.
Iran dai na kallon kasancewar Amurka a yankin a matsayin barazana ga zaman lafiya da tsaro.
A wani labarin na daban mai kama da wannan kwamitin sulhu na MDD ya bukaci sassan kasar Afghanistan da su dakatar da ricikin a tsakaninsu, da kuma kafa wata sabuwar gwamnatin da za ta iya kunshi kowa da kowa, da kuma kare hakkin mata.
A Sanarwar da ya fitar bayan taron da ya gudanar kan kasar ta Afghanistan, kwamitin ya nuna cewa, ya kamata a kare tsaron al’ummomin kasar da na sauran kasashen duniya.
A sa’i daya kuma, kwamitin ya jaddada muhimmancin yaki da ‘yan ta’adda a kasar, domin magance hare-haren da za a iya kai ga sauran kasashen duniya.
A jawabin farko da ya gabatar tun bayan da kungiyar Taliban ta kwace iko, shugaba Joe Biden na Amurka, ya gargadi kungiyar Taliban da cewa duk wani hari a yayin da ake saka da kwashe mutane, Amurka za ta mayar da martani mai karfi kuma cikin gaggawa.
Biden, wanda ke shan suka game da matakin janye dakarun na Amurka a Afghanistan, ya ce baya nadamar matakin da ya dauka, hasali ma ba zai sauya matsayinsa ba.