Shugaban sashen lafiya na majalisar dinkin duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus ya bayyana cewa, sakamakon rashin wadataccen tsarin kula da lafiya da rashin isar taimakon gaggawa a Gaza hakan ya maida gazan wadin mutuwa.
Kungiyar agaji da Red Cresent ta bayyana yiwuwar mawuyacin yanayi a asibitin Khan Yunus idan Isra’ila bata kawo karshen gewayewar da tayiwa asibitin ba fiye da kwanaki talatin.
Mutanen Gaza basu da wadataccen abincin da za su ci kamar yadda Ismail shugaban ofishin yada labaran gwamnati a Gaza ya tabbatar.
Daga ranar 7 ga watan Octoba zuwa yanzu an kashe fiye mutane falasdinawa 29,313, a yayin da wa su 69,333 suka ji raunuka mabambanta, kamar yadda ma’aikatar lafiya ta tabbatar.
Ko majalisar dinkin duniya dole ta tsayar da bada taimakon abinci a Gazan sakamakon hare harden Isra’ila da kuma turereniyar masu bukatar abincin.
A gefe guda kuma gwamnatin amurka na kokawa da Yemen sakamakon matakan da ‘yan houthi na Yemen din ke dauka na hana jiragen dake zuwa Isra’ila wucewa.
Al-Jazeera ta rawaito mai magana da yawun fadar amurka na cewa, ‘yan houthi na ayyuka ne kamar wasu ‘yan ta’adda kuma hare hare da suke kaiwa jiragen ruwa yana kara lalata al’amura ne kuma baya wani taimakon falasdinawa.
Su dai ‘yan Houthi na Yemen suna kai hare haren a Gulf sea da kuma Red sea domin nuna rashin amincewar su da kisan kiyashin da Isra’ila keyi a kan falasdinawa.
A daya bangaren kuma yahudawa sun farmaki mutanen falasdin a kauyen Asira al-Qibliya a kudancin Nablus, inda suka dingi jifa da duwatsu, suka raunata mutum daya sa’annan sukayi kokarin bankawa wani gida wuta, kamar yadda kamfanin yada labarai na Wafa News ya rawaito.
Rahotonni ma dai daga majoyoyin cikin gida da kuma Wafa News sun tabbatar da farmake farmake a wasu gurare kusa bakwai duk Gaza din.
Jaridar Al-Jazeera dai kuma ta rawaito yadda motocin daukan kaya ke ta jira a mashigar Rafah ba tare da sun samu isa Gaza domin kai kayan tallafin jinkai ba.
See Also: Amurkawa Na Bakin Cikin Dawowar Trump
Kamar yadda majoyoyin Majalisar dinkin duniya suka tabbatar motoci hudu ne kawai suka samu wucewa daga ranar laraba.