Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra’ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
Shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya ce akwai bukatar kasashen Musulmi su daina hulda da Isra’ila. Hoto/Reuters
1235 GMT — Iran ta bukaci kasashen Musulmi su daina huldar kasuwanci da Isra’ila
Shugaban Addini na Iran Ayatollah Ali Khamenei ya bukaci kasashen Musulmi da su daina duk wata hulda ta kasuwanci da Isra’ila, ciki har da cinikin man fetur.
Iran din ta bayyana haka ne sakamakon irin hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa Gaza.
“Dole ne gwamnatocin Musulunci su dage kan a daina aikata wadannan laifukan,” kamar yadda Khamenei ya shaida wa taron dalibai a Tehran.
“Kada kasashen Musulmi su rinka hada kai ta fannin tattalin arziki da masu tsatsauran ra’ayin Yahudawa,” in ji shi, inda ya yi kira da a daina kasuwancin man fetur da abinci da su.
1150 GMT — Isra’ila ta sanar da tura jiragen ruwanta na yaki Tekun Bahar Maliya
Rundunar Sojin Isra’ila a ranar Laraba ta sanar da tura jiragen ruwa na yaki zuwa Tekun Bahar Maliya, inda ta ce ta yi hakan ne saboda tsaro.
A shafin X, rundunar sojin Isra’ila ta wallafa hotunan jiragen ruwan nata a Bahar Maliya, wanda tura su na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ilar ke ci gaba da kai hare-hare cikin Gaza.
0920 GMT — Isra’ila ta sake katsa hanyoyin sadarwa da intanet a Gaza
Isra’ila ta sake katse hanyoyin sadarwa da na intanet baki daya a Zirin Gaza da safiyar Laraba, kamar yadda kamfanin sadarwa na Paltel ya koka.
Kamfanonin da ke sa ido kan intanet na duniya sun tabbatar da sake batun sake katse intanet din a Zirin na Gaza.
A ranar Lahadi ne kamfanin na Paltel ya tabbatar da dawowar sabis din a hankali a Gaza.
0852 GMT — Kasashen duniya sun soma janye jakadunsu daga Isra’ila
Kasar Bolivia a ranar Talata ta ce ta yanke huldar dilfomasiyya tsakaninta da Isra’ila sakamakon irin harin da take kai wa Gaza.
Haka kuma kasashen Colombia da Chile su ma sun yi wa jakadunsu kiranye domin tuntuba.
Duka kasashen sun nemi a tsagaita a yakin da ake yi inda kasashen Mexico da Brazil da ke yankin Latin America su ma suka yi kira kan tsagaita wutar.
Source: TRT HAUSA