Isra’ila ta kwashe kwana 38 tana luguden wuta a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 11,100, ciki har da mata da kananan yara fiye da 8,000, tun bayan da Hamas ta kai mata harin ba-zata ranar 7 ga watan Oktoba.
Isra’ila ta kashe ma’aikatan Majalisar Dinkin Duniya sama da 100 a hare-haren da take kai wa Gaza.
0421 GMT — Majalisar Dinkin Duniya na alhinin rasuwar ma’aikatanta a Gaza
An yi kasa-kasa da tutocin Majalisar Dinkin Duniya a ofisoshinta da ke fadin nahiyar Asiya, sannan ma’aikata sun yi tsit na minti daya domin tunawa da abokan aikinsu da Isra’ila ta kashe sakamakon luguden wuta a Gaza.
An yi kasa-kasa da tutocin masu launin shudi da fari da misalin karfe 9:30 na safe a agogon biranen Bangkok, Tokyo da Beijing, kwana guda bayan Majalisar Dinkin Duniya ta bayar da rahotanni na “mutuwar mutane da dama tare da jikkatar wasu” a hare-haren da Isra’ila ta kai a ofisoshinta da ke Gaza.
Hukumar Bayar da Agaji ga Falasdinawa ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNRWA) ranar Juma’a ta ce an kashe ma’aikatanta fiye da 100 tun lokacin da Isra’ila ta kaddamar da hare-hare a Gaza.
0025 GMT — Netanyahu ya nuna alamar tattaunawa da Hamas don sako wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza
Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya nuna alamun cewa za a kulla yarjejeniya da kungiyar Hamas domin yiwuwar sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.
“Ina ganin idan ban yi magana sosai a kan batun ba, za a fi samun damar tabbatar da aukuwarsa,” a cewar Netanyahu a hira da kafar watsa labaran Amurka ta NBC News.
Da yake bayar da amsa kan ko ya san inda mutanen da aka yi garkuwa da su suke a halin yanzu, sai Netanyahu ya ce: “Mun san abubuwa da dama, amma ba na so na yi magana fiye da hakan”.
Firaiministan Isra’ila ya kara da cewa dole ne duk wata yarjejeniya ta kasance tana kunshe da “tursasawa, wato tursasawa irin ta sojoji”.
An dauki wannan hoto ne a yankin Sderot da ke kan iyakar Isra’ila da Gaza da safiyar yau 13 ga watan Nuwamba, 2023, inda yake nuna yadda dakarun Isra’ila suke luguden wuta a yankin. / Hoto: AFP
0000 GMT — Hamas ta yi kira a sa baki don shigar da fetur asibitocin Gaza
Kungiyar fafutukar kare hakkin Falasdinawa ta Hamas ta yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da sauran kasashen duniya su “gaggauta sanya baki don kawo fetur Gaza yadda asibitoci za su ci gaba da aiki.”
Ta fitar da sanarwa domin martani ga ikirarin da sojojin Isra’ila suka yi cewa ta ki karbar fetur domin amfani da shi a Asibitin Al Shifa da ke Gaza.
Kakakin rundunar sojin Isra’ila Avichay Adraee ranar Lahadi ya wallafa sako a shafin X da ke cewa sun bayar da lita 300 na fetur ga Asibitin Al Shifa amma Hamas ta hana jami’an asibitin karba. Sai dai Hamas ta bayyana wannan kalami a matsayin “karya.”
“Hamas ba ta cikin masu gudanar da Asibitin Al Shifa, sannan ba ta cikin asibitin, kana Asibitin yana karkashin kulawar Ma’aikatar Lafiya ta Falasdinu, wadda ke tafiyar da ayyukansa na gudanarwa da na yau da kullum,” in ji kungiyar.
Source: IQNAHAUSA