Wannan shafi yana kawo muku sabbin bayanai a ranar Laraba, 8 ga watan Nuwamba, kan hare-haren da Isra’ila ke kai wa Gaza bayan Hamas ta kutsa kai Isra’ila inda ta kai mata hare-haren ba-zata a ranar 7 ga watan Oktoba.
Asibitoci na fama da tsananin karancin manfetur a Gaza. Hoto/Reuters
0855 GMT — Iraki ta ba asibitocin Gaza kyautar lita miliyan 10 ta fetur
Gwamnatin Iraki ta bayar da kyautar lita miliyan goma domin amfanin janaretoci a asibitoci a Zirin Gaza a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hari Falasdinu.
Firaiministan Iraki, Mohammed Shia al-Sudani ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.
Sanarwar ba ta bayyana ranar da za a kai man fetur din ba ko kuma yadda za a shigar da shi cikin Gaza duk da kawanyar da aka yi.
Har yanzu Isra’ila ba ta bari an shiga da man fetur cikin Gaza ba tun bayan soma wannan rikicin.
0800 GMT — Sojin Isra’ila sun kama ‘yan jarida biyu a birnin Hebron
Rundunar sojin Isra’ila ta kama ‘yan jarida biyu a Gabar Yamma da Kogin Jordan a ranar Laraba.
Wadanda suka shaida lamarin sun sanar wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa an kama Mohamed al-Atrash da Amer Abu Arafa bayan sojojin na Isra’ila sun kai samame gidajensu da ke birnin Hebron inda suka gudanar da bincike.
Sama da ‘yan jarida 36 aka kashe tun bayan soma wannan rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa. Hoto/Reuters
Rahotanni sun kuma ce sojojin na Isra’ila sun tsare wasu jama’ar a Hebron da Bethlehem da Ramallah da Nablus da Qalqilya da Jericho.
0325 GMT — Saudiyya ta ce za ta karbin bakunci taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmai don tattauna yakin Gaza
Isra’ila na ci gaba da luguden wuta a Gaza. Hoto: Reuters
Ministan zuba jari na Saudiyya ya ce nan da kwanaki masu zuwa kasar za ta karbi bakuncin taron koli na kasashen Larabawa da kasashen Musulmai domin tattaunawa kan yakin Isra’ila da Falasdinu.
“Za mu gani a cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, Saudiyya ta kira wani taron gaggawa na Larabawa a Riyadh,” in ji ministan zuba jari na Saudiyya, Khalid Al-Falih, a taron Bloomberg New Economy Forum a Singapore.
“Nan da ‘yan kwanaki za ku ga kasar Saudiyya na gudanar da taron kasashen Musulmai,” in ji shi.
“A cikin kankanin lokaci, makasudin gabatar da wadannan tarukan guda uku da sauran tarukan karkashin jagorancin Saudiyya shi ne a kai ga warware rikicin cikin lumana.”
Kamfanin dillancin labaran Etemad ya rawaito cewa, shugaban kasar Iran Ibrahim Raisi zai tafi Saudiyya a ranar Lahadi mai zuwa don halartar taron kolin Ƙungiyar Hadin kan Ƙasashen Musulmai, wadda ita ce ziyarar farko da wani shugaban kasar Iran ya kai tun bayan Tehran da Riyadh suka kawo karshen rashin jituwar da aka shafe tsawon shekaru ana yi karkashin wata yarjejeniya da China ta kulla a watan Maris.
0300 GMT — An yi tir da kalaman Rashida Tlaib ta yi a kan Isra’ila saboda yaƙin Gaza
Rashida Tlaib ita ce Ba’amurkiya kuma Bafalasɗiniya ɗaya tilo a Majalisar Wakilan.
Majalisar Wakilan Amurka ta kaɗa ƙuri’a don hukunta ‘yar Jam’iyyar Democrat dmai wakiltar Michigan, Rashida Tlaib – Ba’amurkiya kuma Bafalasɗiniya ɗaya tilo a Majalisar – tsawatawar mai ban mamaki.
Kuri’un da aka kaɗa 234-188 na zuwa ne bayan isassun ‘yan jam’iyyar Democrat sun haɗa kai da ‘yan Republican don tsawatarwa Tlaib, a wani hukunci wanda daga irinsa sai kora daga majalisar.
‘Yar majalisar da ta shafe wa’adi uku ta daɗe tana shan suka kan ra’ayoyinta kan rikicin da aka kwashe shekaru da dama ana yi a Gabas ta Tsakiya.
Dan majalisar wakilai na Republican Rich McCormick na Georgia ne ya ingiza ɗaukar wannan matakin a matsayin martani ga abin da ya kira kambama kalaman nuna ƙyama da Tlaib ke yi. Ya ce ta “yi ƙarairayi da dama a game da babbar ƙawarmu, Isra’ila, da harin da aka kai ranar 7 ga Oktoba.”
Tlaib, wacce wasu ‘yan jam’iyyar Democrat ke goyon bayanta, ta kare matsayinta, tana mai cewa “ba zan yi shiru ba kuma ba zan bar ku sauya maganata ba.”
Tlaib ta kara da cewa sukar da take yi wa Isra’ila a ko da yaushe tana yi ne a kan gwamnatin ƙasar da kuma jagorancinta a karkashin Firayim Minista Benjamin Netanyahu.
“Yana da mahimmanci a dinga raba batun mutane da na gwamnati,” in ji ta. “Ra’ayin cewa sukar gwamnatin Isra’ila abu ne na ƙyamar Yahudawa abu ne mai hatsarin gaske. Kuma an yi amfani da shi wajen rufe bakunan mutane daban-daban na kare hakkin bil’adama a fadin kasarmu.”
Source: TRTAfrica