Yaƙin Isra’ila a Gaza ya shiga kwana na 247 inda ya kashe aƙalla Falasɗinawa 37,084 — kashi 71 daga cikinsu mata ne da yara da jarirai — sannan mutum 84,494 sun jikkata, a cewar jami’ai.
Gantz, wanda tsohon soja ne, ya shiga gwamnatin Netanyahu jim kaɗan bayan harin ba-zata da ƙungiyar Hamas ta kai Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata./Hoto: Reuters
Ministan Ma’aikatar yaƙi ta Isra’ila Benny Gantz ya sauka daga muƙaminsa
Ministan Ma’aikatar yaƙi ta Isra’ila Benny Gantz ya sauka daga muƙaminsa tare da ficea daga gwamnatin-gaggawa ga Firaminista Benjamin Netanyahu a yayin da suka kwashe watanni takwas suna luguden wuta a Gaza.
“Muna cike da baƙin-cikin ficewa daga gwamnatin haɗin-kai,” in ji Gantz a wani jawabi da ya gabatar a gidan talbijin.
Kazalika Gantz ya yi kira ga Benjamin Netanyahu ya gudanar da zaɓe “nan ba da jimawa ba”.
Gantz, wanda tsohon soja ne, ya shiga gwamnatin Netanyahu jim kaɗan bayan harin ba-zata da ƙungiyar Hamas ta kai Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoban da ya gabata.
Wani asibitin Gaza ya samu yara 50 da ke fama da rashin isashen abinci
Wani asibiti a arewacin Gaza ya ce a cikin mako daya kacal ya samu yara 50 Falasɗinawa waɗanda ke fama da rashin isashen abinci.
Hossam Abu Safiya wanda shi ne daraktan Asibitin Kamal Adwan, shi ya bayar da rahoton waɗannan alƙaluma a wata sanarwa da ya fitar.
“Ɓangaren lafiya na Gaza ya kasance wurin da Isra’ila ke hari, amma muna ƙoƙarin ci gaba da aikin samar da lafiya a ko yaya ne saboda ƙarancin fetur,” kamar yadda ya bayyana.
Ya bayyana cewa “yanayin bala’i ne,” yana mai jaddada cewa “yunwa na neman mamaye Gaza.”
DUBA NAN: Yawan Falasɗinawan da Isra’ila ta kashe a Gaza ya kai 36,654 — Ma’aikatar Lafiya
Sakamakon yakin da ake ci gaba da yi da kuma takunkumin da Isra’ila ta saka, akw
ai ƙarancin abinci, ruwa, magani, da man fetur a Gaza.