Ministan harkokin wajen kasar china,Mista Qing Gang ya bayyana cewa, bai kamata nahiyar Afirka ta zama dandalin husumar manyan kasashen duniya ba, a cewar sa ya kamata ne nahiyar ta Afirka ta zama dandalin hadin kai domin cigaba.
Mista Gang ya bayyana hakan ne ranar laraba a lokacin daya ziyarci bude ofishin kungiyar lafiya ta pan-African a birnin Adis Ababa.
Minsitan ya kuma bayyana hadin kan kasar chana da nahiyar Afirka a bangaren tsaro da kuma cigaban tattalin arziki.
“Babu wata kasa ko wasu mutane da suka isa su sanya kasashen Afirka su dauki bangare” Minsitan harkokin wajen Chanan ya bayyana haka a lokacin gabatar da taron manema labarai wanda ya gudanar tare da shugaban kungiyar kasashen Afrika Moussa Faki Mahamat.
“Ya kamata Afirka ta zama babban wajen hadin kai ba wajen zakaran gwajin dafin manyan kasashen duniya ba” Yace kuma ya kara da cewa “Gudummawar China wajen cigaban Afirka yafi dutse karfi”.
Gang wanda yayi zaman ambasadan Chana a amurka har zuwa disambar data gabata yanzun yana gabatar da zagayen aikin sa na farko a kasashen duniya matsayin sa na sabon minsitan harkokin wajen Chana.
A nasa bangaren Moussa Faki Mahamat ya bayyana cewa rashin samun cikakken wakilcinn Afirka a kwamitin tsaro Lamari ne mai sosa rai” lura da cewa mafi yawancin lamurran tsaro da ake tattaunawa a majalisar sun shafi Afirka ne.
“Ba karbabben abu bane ace wasu su dauki matsaya dangane da wasu. Babu adalchi muna bukatar sabon tsari a matsakin kasa da kasa (Duniya) wanda zai girmama muradun kowa da kowa” Kamar yadda Moussa Faki Mahamat yace.
Shugaban kungiyar kasashen Afirkan ya bayyana cewa “Afirka taki yarda ta zama wata cibiyar musayar tasiri da karfin fada aji… Muna shirye muyi aiki tare da kowa amma dole a girmama muradan mu. Hadin kanmu da kasar Chana a kan wadannan muradai ya doru.