Gwamnan jihar Kano dake Najeriya Abdullahi Umar Ganduje ya zabi mataimakin sa Nasir Gawuna a matsayin wanda zai gaje shi a zaben shekara mai zuwa.
Bayanan dake fitowa daga Jihar sun ce Ganduje ya zabi Gawuna ne wajen taron masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC da aka gudanar a Jihar dangane da zaben mai zuwa.
Mahalarta taron sun kuma amince da tsohon kwamishinan kananan hukumomi Murtala Sule Garo a matsayin wanda zai marawa Gawuna baya a zaben mai zuwa.
Majiyoyi daga wajen taron sun ce sanda jiga jigan jam’iyyar suka taka rawa sosai wajen sanya Garo janyewa daga neman takarar gwamnan domin komawa mataimakin Gawuna.
Masu sanya ido akan siyasar Kano sun ce Gawuna ya taka rawa sosai wajen ci gaban da jihar ta samu a bangaren noma da samar da abinci tare da goyawa Ganduje baya wajen jagorancin jihar.
A wani labarin na daban Kungiyar Masu taimakawa likita da unguwar zoma a Najeriya tace tayi asarar mambobin ta sama da dubu11 da suka bar kasar zuwa kasashen da suka ci gaba a cikin shekaru 3 domin samun rayuwa mai inganci.
Shugaban kungiyar Michael Nnachi ya bayyana haka dangane da bikin duniya na makon masu aikin taimakawa likitan, inda ya danganta matsalar da aka samu da rashin ingancin yanayin aikin da kuma wahalar da suka sha sakamakon barkewar annobar korona.
Nnachi wanda yace masu irin wannan aikin akalla 5,000 suka rasa rayukan su a kasashen duniya sakamakon annobar korona a shekarar 2020, yace Najeriya na matukar fama da karancin masu aikin taimakawa likitocin.
Shugaban kungiyar ya bukaci gwamnatin Najeriya ta sake fasalin aikin wajen inganta shi yadda mambobin su zasu daina tserewa zuwa kasashen da suka ci gaba domin samun rayuwa mai inganci.