Al’ummar Gambia na kada kuri’ar zaben ‘yan majalisar dokokin kasar a wannan Asabar, zaben da wasu ke ganin ka iya karfafawa shugaba Adama Barrow ikonsa bayan da ya sake lashe zabe a shekarar bara.
Sai dai daga cikin kujerun ‘yan Gambia za su zabi 53 uku ne, yayin da Shugaba Barrow zai bayyana sunayen ragowar biyar da zai zaba, cikinsu har da shugaban majalisar.
Za a bude rumfunan zabe da karfe 8:00 na safe sannan a rufe da karfe 5 na yamma.
A wani labarin na daban Sojojin Burkina Faso Akalla 12, da kuma wasu jami’an tsaron sa-kai 4 ne suka rasa rayukansu, sakamakon wani hari da ‘yan ta’adda suka kai musu, a jiya Juma’a.
Bayanai sun ce an kai harin ne a kan wani karamin barikin soji mai suna Namissi-guima da ke arewacin kasar.
Arewacin Burkina Faso dai ya rikide zuwa cibiyar hare-haren ‘yan ta’adda masu ikirarin Jihadi wadanda suka fara kai hare-haren cikin kasar daga makwabciyar ta Mali a shekarar 2015.
Alkaluman baya bayan nan kuma sun nuna cewar, zuwa yanzu tashin hankalin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan dubu 2,000, tare da raba wasu kusan miliyan 2 da muhallansu.
Tun cikin watan Janairun da ya gabata, Burkina Faso ta kasance a karkashin mulkin soja da Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba ke jagoranta, bayan juyin mulkin da sojojin suka yi saboda gazawar zababben shugaban kasar, Roch Marc Christian Kabore wajen murkushe matsalar ta’addanci.