Gwamnatin Najeriya ta bada umarnin gaggauta rufe ofisoshin gwamnati da ke Abuja daga karfe 1 na ranar wannan Talata, domin nuna goyon baya ga wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin duniya da Super Eagles za ta kara da Black Stars ta Ghana.
Najeriya da Ghana zasu fafata a filin wasa na Moshood Abiola da ke Abuja a yammacin wannan Talata, a wasan da ake saran yayi zafi tsakanin kasashen biyu dake hamayya na shekaru 71 da fafatawa 58, bayan haduwarsu ta ranar Jumma’a Kumasin Ghana aka karkare mintuna 90 babu wanda ya ci wani.
A wani labarin na daban kuma Fim din Nomadland da ke nuna yanayin rayuwar tsofaffin Amurkawa masu gararamba a cikin kwarababbiyar motar akori-kura, ya lashe lambar yabo ta Oscar saboda kyawun daukar hotonsa.
Kazalika ta zama mace ta biyu a tarihi da ta lashe kyautar a matsayinta ta mai bada umarni bayan Kathryn Bigelow wadda ta fara bude babin irin wannan tarihin a shekaarr 2010, lokacin da aka karrama ta saboda fim din “The Hurt Locker.”
Zhao ‘yar asalin China ce, amma kafafen yada labarai na kasarta ba su yada labarin nasararta ba.
A can baya, Zhao ta taba janyo cece-kuce a China saboda yadda ta caccaki kasarta a wata hira da ta yi da manema labarai.
A bangare guda, Frances McDormand ita ma ta samu lambar yabo ta gwarzuwar jaruma, yayin da Anthony Hopkins ya lashe kyautar a matsayinsa na gwarzon jarumi.
Hopkins mai shekaru 83, ya zama jarumin fina-finai mafi tsufa a tarihi da ya lashe kyautar ta Oscar.