Gabashin Ukraine Rasha Ta Yi Kira Ga Sauren Kasashe Su Yi Koyi Da Ita.
Kasar Rasha ta yi kira ga sauren kasshen duniya su yi koyi da ita, ta hanyar amincewa da jamhuriyar Lugansk da kuma jamhuriyar Donetsk na gabashin Ukraine a matsayin kasashe masu cin gashin kansu.
Ministan harkokin wajen Rashar ne Sergio Lavrov, ya yi wannan kiran, a daidai lokacin da kasashen turai da Amurka ke cewa sunan nan suna shirin kakaba takunkumai masu tsari kan kasar ta Rasha game da matakin da ta dauka.
A jiya Litinin ne shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin ya rattaba hannu kan wasu umarni biyu dake nuna amincewa da samun ’yancin kan “jamhuriyar Lugansk (LPR)” da “jamhuriyar Donetsk (DPR)” a matsayin kasashe masu cin gashin kansu.
A wani bikin da aka gudanar a fadar Kremlin, Putin ya kuma sanya hannu kan yarjejeniyar kawance, da hadin gwiwa, da cudanyar tallafawa juna tsakanin Rasha da LPR da kuma DPR, tare da shugabannin jamhuriyoyin biyu, kamar yadda fadar Kremlin ta sanar.
Rikicin tabarbarewar yanayin tsaro a kasar ta yankin Turai na faruwa ne sakamakon fadada ikon kungiyar hadin gwiwar tsaro ta NATO a gabashin kasar, lamarin da ya haddasa rashin jituwa a tsakaninta da shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.