Fitaccen dan damben boxing a duniya dan asalin Birtaniya Tyson Fury, ya bayyana cewa sai an biya shi fam miliyan 500 muddin ana bukatar ya sake komawa fagen wasan dambe.
Fury mai shekaru 33, na cigaba da nanata cewar zai yi ritaya daga wasan damben boxing bayan da ya samu nasarar doke Dillian Whyte a filin wasa na Wembley a cikin watan Afrilu.
Gwarzon gasar damben ajin masu nauyi ta WBC ya yi wa magoya bayansa bazata a lokacin da ya bayyana matakinsa na yin ritaya, sai dai daga bisani ya ce a shirye yake ya koma fili domin fafata wasa na musamman da Anthony Joshua, idan har za a biya shi fam miliyan 200.
A halin yanzu kuma Tyson Fury ya daga darajar kudin da ya nema zuwa fam miliyan 500.
A wani labarin na daban fitaccen dan damben boxing ajin masu nauyi Anthony Joshua dan Ingila, ya yi watsi da rahotannin cewa ya amince da yarjejeniyar karbar fam miliyan 15 kwatankwacin Yuro miliyan 18 don janyewa daga shirin sake karawa da Oleksandr Usyk na kasar Ukraine.
A watan Satumban shekarar bara ne dai Usyk ya kwace dukkanin kambun Joshua na WBA da IBF da kuma WBO, bayan lallasa Joshuan da yayi a fafatawar da suka yi.
Rashin nasarar da Joshua ya yi a karon battarsa da Oleksandr Usyk, itace karo na biyu da fitaccen dan damben boxing din ya fuskanta tun bayan ficen da yayi.
A baya bayan nan ne kuma kafafen yada labarai da dama ciki har da na kasar Birtaniya suka wallafa rahoton cewa, Joshua ya yarda Usyk ya biya fam miliyan 15, domin janyewa da shirin sake fafatawar da aka tsar za su yi, labarin da fitaccen dan damben dan asalin Najeriya ya bayyana a matsayin mara tushe.
A karshen watan Satumban da ya gabata, fitaccen dan damben boxing na Ingila ya kafe kan cewa zai iya fafatawa da Tyson Fury wani fitaccen dan damben na boxing wani lokaci nan gaba kadan, koda kuwa ba tare da kambunansa guda uku na duniya ba.