Furusunoni Falasdinawa Sun Fara Yajin Cin Abinci Na Gama- Gari A Dukkan Kurkukun Isra’ila.
A wani mataki na nuna rashin amincewa da cin zarafin fursunoni falasdinawa da Isra’ila take yi da dama daga cikin Falasdinawa dake tsare a gidan kurkukun Isra’ila sun fara yajin aikin cin abinci na gama gari, mahukumtan isra’ila na firgita fursunoni da hakan keta yarjejeniyar da aka cimma a watan maris da rattaba hannun tsakanin gwamantin isra’ila da kungiyar kare hakkin fursunoni falasdinawa.
Kwamiti koli na taimakon gaggawa ga fursunoni falasdinawa ya fitar da sanarwar a ranar Asabar cewa fursunoni da dama za su fara yajin cin Abinci a ranekun litinin da Laraba kafin su fara yajin aiki n agama gari a dukkan gidajen yarin Isra’ila.
Matakin baya bayan nan yana zuwa ne bayan da mahukumtan gidan yari Isra’ila suka ki mutunta jayejeniayr maris da aka cimma matsaya a kai, inda sam da fursunoni 500 ne suka kauracewa zaman kotun soji tun farkon wannan shekarar , ciki har da kauracema sauraron batun sabunta umarnin ci gaba da rikesu a hukumance da kuma zaman da kotun koli ta isra’ila ke yi.
Fursunoni falasdinawa na ci gaba da shiga yajin cin abinci a fili ne domin nuna bacin ransa game da ci gaba da tsare su da ake yi, hukumomin gidan yarin Isra’ila na tsare da falasdinawa cikin mummunan yanayi ba tare da kula da mataken tsafta ba, kuma suna fuskantar Azabatarwa da tsangwama da danne hakkokinsu.