Fursunonin Falasdinawa Za su Fara Gudanar da Yajin Cin Abinci Na Gama gari A Gidajen Kurkukun Isra’ila.
Hukumar kula da fursunonin falasdinawa a gidajen kurkukun isra’ila ta bayyana cewa a gobe litinin ne da dama daga cikin Fursunoni da ke tsare a gidan kurkukun Isra’ila za su fara zanga-zanga da yajin kin cin abinci domin nuna rashin amincewarsu da ci gaba da tsaresu a gidan yari ba bisa doka ba.
Wannan matakin yana zuwa ne bayan d a mahukumtan gidajen yarin israila suka ki mutunta yarjejeniyar maris da aka kulla inda suka ci gaba da Azabtar da fursunoni da ake tsare da su, musamman wadand aka yi musu daurin rai da rai.
Akalla fursunoni guda 500 ne suka ki halartar sauraran zaman koton soji tun daga farkon wannan shekarar, da ya hada da kauracewa zaman sabunta umarni tsaresu a gwamnatance da kuma sauraran shari’oin daukaka kara a kotun kolin Isra’ila.
Dubban falasdinawa ne Isra’ila ke tsare da su a gidajen yari , hukumar kare hakkin bil adama ta zargeta da keta dukkan hakkoki da yanci da yarjejejniyar Janeva ta basu, sun ce tserewa a gwamnatance ya sabawa hakkin bin diddigi, domin ana boye takardun fursuna da ake tsare da shi, alhali ana ci gaba da tsareshi na dogon lokaci ba tare da tuhuma ko shari’a ba.