Wasu ‘yan bindiga sun bude wuta kan mai uwa da wabi a taron kade-kade da raye-raye a birnin Miami na jihar Florida da ke Amurka, inda akalla aka tabbatar da mutuwar mutane biyu, yayin da kimanin 20 ke cikin mawuyacin hali.
Harin ya auku ne a harabar wani katafaren dakin gudanar da bukukuwa a wani dandali da ke birnin Miami, inda akasari mutanen kasar Cuba masu rufan asiri ke rayuwa.
Rahotanni sun ce, maharan sun sanya manyan riguna tare da rufe fuskokinsu kafin tarwatsa taron jama’ar da harsashai.
Majiyar ‘yan sanda ta ce, ‘yan bindigar sun iso ne a cikin wata motar SUV kirar Nissan Pathfinder, inda mutane uku daga cikinta suka fito, sannan suka fara bude wuta kan taron jama’ar.
Tuni ‘yan bindigar suka tsere bayan aika-aikar, kuma kawo yanzu babu cikakken bayani game da makasudin kadddamnar da farmakin kan mahalarta bikin.
A halin yanzu, mutane 20 da suka samu raunin harsasahai a harin na kwance a asibiti rai-kwa-kwai mutu-kwakwai a cewar ‘yan sanda.
Jami’an tsaro na neman hadin kan al’ummar yankin wajen farautar wadannan mahara.
Amurka na fama da matsalar hare-haren bindiga, lamarin da ke haddasa asarar dubun dubatan rayuka a duk shekara a kasar.
A wani labarin na daban mutane da dama sun rasa rayukansu, yayin da wasu suka jikkata sakamakon wani harin bindiga da aka kaddamar a ginin ma’ajiyar kayayyaki da ke arewacin Baltimore na Amurka.
Rahotanni na cewa, wata mace ce ta kaddamar da harin bindigar kan dandazon jama’a, abin da ba a saba gani ba a kasar cewa, mace ta kai irin wannan farmakin.
Ko da dai jami’an ‘yan sanda na kan aikin tantance hakikanin jinsin maharin ko kuma ‘yar bindigar.
Shugaban rundunar ‘yan sandan yankin Harford da ke Maryland, Jefferey Gahler ya tabbatar da jikkatar mutane da dama da kuma salwantar rayuka.
Gahler ya ce, ana ci gaba da tsare ‘yar bindigar daya tilo wadda ke cikin mawuyacin hali a wani karamin asibiti.
Jami’in ya ce, akwai yiwuwar matar ce ta raunata kanta da kanta domin kuwa babu wani dan sanda da ya yi harbi da nufin martani ga harin.
Kafofin yada labaran Amurka sun rawaito cewa, akalla mutane uku aka rasa a harin wanda aka kai a cibiyar rarraba magunguna ta Rite Aid da ke ginin na ma’ajiyar kayayyaki.
Tuni aka baza jami’an Hukumar Binciken Manyan Laifuka ta Amurka FBI a wurin da harin ya auku.
Ana yawaitar samun hare-haren bindiga kan dandazon al’umma a Amurka, yayin da kundin tsarin mulkin kasar ke kare hakkin mallakar bindigar.