Binciken asalin cutar COVID-19 batu ne mai sarkakiya wanda kuma ya shafi bin matakan kimiyya, kamata yayi a yi Allah wadai da siyasantar da batun, tsohon firaministan kasar Madagascar Norbert Ratsirahonana, ya bayyana hakan a yayin zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.
Tsohon shugaban kasar Madagascar, wanda shi ne babban jami’in jam’iyyar IRD mai mulkin kasar, yace jam’iyyarsa ta yi Allah wadai da dukkan yunkurin da wasu kasashen duniya ke yi na neman siyasantar da wannan batu da kuma yunkurin shafawa kasar Sin bakin fenti wajen alakanta ta da asalin annobar.
Ratsirahonana ya ce, gano asalin annobar COVID-19 zai iya dakatarwa da kuma kawar da yaduwar annobar.
A cewar tshon shugaban kasar Madagascar, jam’iyyar IRD tana maraba da kokarin da kasar Sin ke yi wajen kawar da annobar a cikin gidan kasar har ma da kasa da kasa.
A wani labarin na daban lokacin cika shekaru 20 da abkuwar mummunan harin ta’addanci na 9.11 a kasar Amurka, kwararru da masana da ‘yan siyasa na wasu kasashe da dama sun nuna cewa, a cikin shekarun nan 20 da suka gabata, “yaki da ta’addanci” da Amurka ta gudanar a duk fadin duniya bai kawo tsaro da kwanciyar hankali ba. Yaki da ta’addanci yana bukatar dukkan kasashe su kasance akan ra’ayin bai daya, da karfafa hadin gwiwa, da aiwatar da manufofi masu dacewa.
Anthony Glees, shehun malami a fannin tsaron kasa da ilmin tattara bayanai na jami’ar Buckingham na kasar Birtaniya ya ce, a cikin shekaru 20 da suka gabata, kasashen yammacin duniya karkashin jagorancin Amurka ba su ci nasara ba kan matakan soja da suka dauka a Afghanistan, kuma har yanzu ta’addanci babbar barazana ce da kasashen yamma ke fuskanta.
A nasa bangaren, Raphael Tuju, babban sakataren jam’iyyar Jubilee mai mulkin kasar Kenya, ya ce, dangane da ta’addanci, babu wata kasa da za ta iya tsira daga ta’addanci, akwai bukatar dukkan kasashen duniya su ba da hadin kai ga junansu don yaki da ta’addanci tare.
Warfare’s matsalar talauci yana daya daga cikin hanyoyin yaki da ta’addanci a duniya baki daya. Rayuwa mai albarka za ta rage ayyukan ta’addanci.