Firaministan rikon kwaryar Libya Abdulhamid Dbeibah ya yi rajistar shiga takarar zaben shugaban kasar da za a yi a watan gobe, abinda ya sa shi cikin jerin yan takarar da suka hada da ‘dan tsohon shugaban kasa Moammar Ghadafi, wato Seil al-Islam.
Dbeibah mai shekaru 62 da ya fito ne daga yankin Misrata, ya zama firaministan rikon kwarya ne a watan Fabarairu domin shirya zaben kasar.
A ranar 24 ga watan Disamba mai zuwa ake saran gudanar da zaben shugaban kasar Libya, a daidai lokacin da Majalisar Dinkin Duniya ke kokarin kawo karshen tashin hankalin da ya mamaye kasar tun bayan kashe shugaba Moammar Ghadafi a shekarar 2011.
Daga cikin ‘Yan takarar shugaban kasar guda 4 akwai shugaban majalisar dokoki Aguila Saleh da Janar Khalifa Haftar da kuma ‘dan tsohon shugaban kasa Ghadafi, Seif al Islam.
A wani labarin na daban hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya UNHCR ta sanar da kwashe masu neman mafaka ko ‘yan gudun hijira 172 daga inda ake tsare da su a Libya zuwa Jamhuriyar Nijar.
A cikin wata sanarwa da hukumar ta UNHCR ta fitar ta ce da yawa daga cikin wadanda ta kwashe din an tsare su ne a cikin mawuyacin hali a kasar Libya.
Mutanen da aka kubutar dai sun hada da iyalai, da yaran dake tafiya su kadai, har ma da wani jariri da aka haifa makwanni kadan da suka gabata.
Tun shekarar 2011 kasar Libya ta fada cikin rudani da rikici bayan hambarar da gwamnatin Mu’ammar Gaddhafi a shekara ta 2011, inda ta zama mashigar da ‘yan ci rani ke amfani da ita wajen kokarin ketarawa nahiyar Turai.
Sai dai da yawa daga cikin ‘yan ci ranin ana tsare su ne cikin wani yanayi da kungiyoyin kare hakkin dan adam suka yi Allah wadai da su.
A cikin watan Oktoban da ya gabata hukumomin kasar Libya suka janye dokar hana jiragen kwashe ‘yan ci ranin fita daga kasar.