Firaministan Haiti Ariel Henry ya nada sabon ministan shari’a kwana guda bayan ya kori mai gabatar da karar da ya bukaci yi masa tambayoyi saboda zargin da ake masa na hannu wajen kasha shugaban kasa Jovenil Moise.
Kafin wannan nadi, Quitel na rike da mukamin ministan cikin gida tun daga ranar 20 ga watan Yuli.
Nadin da Firaministan yayi ya zo ne yayin da rudani ya mamaye al’ummar Haiti, sama da watanni biyu bayan kisan da aka yi wa shugaban kasa a gidansa na sirri da tsakar dare, ta’addancin da tawagar miyagu dauke da makamai ta aiwatar.
Cikin wata wasika wadda ke matsayin ta 2 da sashen shigar da karar ya gabatarwa gwamnati ya nemi hukumar shige da fice ta kasar ta haramtawa Firaminista Ariel Henry barin kasar a kowanne yanayi.
Wata shaidar baya-bayan nan ta nuna yadda Henry ya yi waya da babban wanda ake zargi da kisan shugaban na Haiti, lokaci kankani bayan farmakin da ya hallaka shugaban.
Wasikar mai dauke da sa hannun babban mai shigar da kara ta kasar ta kuma nemi izinin gurfanar da Firaministan don amsa tuhuma dangane da alakarsa da maharan na ranar 6 ga watan Yuli.
Tun a juma’ar da ta gabata babban mai shigar da karar ya aikewa da Firaministan bukatar ganin ya bayyana gaban kotu jiya talata don amsa tambayoyi da ke matsayin kari kan bayyanarsa gaban mahukuntan kasar sa’o’I kalilan bayan kisan shugaba Moise amma kuma yaki mutunta gayyatar.