Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: A martanin da ya mayar da zaman kotun kasa da kasa ba domin gudanar da bincike kan laifukan wannan gwamnati Firaministan Netanyahu ya ce: Ana zargin mu da kisan kiyashi a lokacin da muke yaki da masu kisan kare dangi!
Firaministan gwamnatin kashe yara kanana ya bayyana cewa: Sojojin Isra’ila su ne sojojin da suka fi da’a a duniya, wadanda suke yin duk wani abu don hana cutar da fararen hula, kuma ana zargin wannan sojojin da kisan kiyashi.
Bidiyon Yadda Netanyahu Ya Nuna Fushinsa Akan Afirka Ta Kudu Da Kotun Kasa Da Kasa
Kamfanin dillancin labaran shafin sadarwa na Ahlul Bayt (AS) na – ABNA – ya habarta maku cewa: Ministan harkokin wajen Iran Amir Abdullahian ya ce: Muna matukar goyon bayan matakin jajircewa da gwamnatin Afirka ta Kudu ta dauka kan gwamnatin sahyoniyawan da ke kashe kananan yara inda ta takai kararta a gaban kotun duniya.
A sashe guda kuma bayan kammala zaman farko na karar da Afrika ta Kudu ta shigar kan gwamnatin sahyoniyawan kan kisan kiyashin da take yi a zirin Gaza a gaban kotun kasa da kasa da ke birnin Hague, Benjamin Netanyahu a fusace da kakkausar murya ya yi martani ga Afirka ta Kudu da kotun tare da kiran sojojin gwamnatinsa. “mafi kyawawan halin kirki Sojojin duniya!
Firaministan yahudawan sahyoniya ya yi iƙirarin cewa: A yau duniyarmu ta juye kuma muna yaƙi da ‘yan ta’adda da makaryata.
Shi ya fusata da karar shari’ar gwamnatin sahyoniyawan ya kara da cewa: muryar munafuncin Afirka ta Kudu ta yi a banza.
Netanyahu ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da kare abin da ya kira “yancin kare kansa da kuma tabbatar da makomarta har zuwa cikakken nasara.”
A mayar da martani ga sauraron karar kisan kiyashin da gwamnatin sahyoniya ta yi a kotun Hague, ya yi da’awar cewa: Sojojin Isra’ila, wadanda su ne sojojin da suka fi da’a a duniya, ana tuhumarsu da laifukan yaki.
Source: ABNAHAUSA