Firaministan na Falasdinu Mohammad ya bayyana sanarwar da Isra’ila tayi na gina sabbin matsugunai wadanda basu a kan ka’ida guda 3000 a matsayin babban kalubalen dake fuskantar kasashen duniya da kuma kawo cikas ga kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta.
Kamar yadda kafar sadarwa ta Al-Jazeera ta rawaito Firaministan ya bayyana cewa, ayyukan Isra’ila sun bayyana bata mutunta dokokin kasa da kasa.
Za dai a soma gina rukunin sabbin matsugunan nan da sati biyu a matsugunin Ma’ale Adumim wanda Isra’ilan ta mamaye a gabashi Kudus.
Kungiyar dake sa ido a kan ayyukan Isra’ila “Peace Now” ta bayyana cewa kasafin kudin Isra’ila na 2024 ya nuna karin sama da dala miliyan dari ga matsugunan.
A wani labarin na daban kuma majalisar dinkin duniya tayi gargadin karuwar yunwa a gaza ta hanyar babbar kungiyar ta mai bada agajin gaggawa ta UNWRA, ana matukar bukatar tallafi yayin da falasdinawa ke cikin mawuyacin hali kuma duniya tana kallo.
Hotunan da kamfanin dillacin labarai na AFP ya raba ya nuna yadda mutanen ke cikin rudani yayin suke kan layin abinci tare da aiwatar da zanga zangar nuna damuwa kan halin da suke ciki a ranar juma’a.
“Dubi muna fama da juna kan shinkafa” Inji wani mazaunin yankin Ahmad Atef Safi, “Ina zamuje?”
Bamu da ruwa ba gari kuma mun gaji ga yunwa, bayan mu da idanun mu sunyi zafi saboda wuta da hayaki, Inji wani mazaunin Jabalia.
Ya kuma bayyana cewa ba zasu iya tsayawa da kafafun su ba saboda gajiya.
Duba Nan: Matasa Sun Wawashe Kayan Abinci A Neja
A wata sanarwa da ta fitar a shafin ta na X hukumar jinkai ta majalisar dinkin duniya OCHA tace idan ba’a samar da wadataccen abinci da ruwan sha da kiwon lafiya da abinci mai gina jiki ba a kwai yiwuwar karuwar yunwa a Gaza.