Ita kanta Uefa ta yiwa hukumar kwallon kafar ta Hungary makamancin hukuncin ta hanyar cin tarar ta yuro dubu 85 da kuma hana ‘yan kallo shiga fili a wasanni 3 duk dai dangane da nuna wariyar amma wannan yayin wasannin Euro 2020 da suka gudana cikin watan yuni zuwa Yuli.
‘Yan wasan da suka gamu da nuna wariyar sun hada da Raheem Sterling da kuma Jude Bellingham wadanda magoya baya suka riga jifa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci yayin wasan kasashen biyu a Puskas Arena wanda Ingilar ta yi nasara kan Hungary da kwallo 3 da nema.
A wani labarin na daban hukumar FIFA ta ce kwamitinta na ladabtarwa yanzu haka ya fara shirye-shiryen hukunta kasashen Argentina da Brazil bayan takaddamar da ta kai ga dakatar da wasansu na neman gurbin shiga gasar cin kofin Duniya a makon jiya.
A cewar Fifa hukuncin zai kasance bisa ga bayanan da jami’anta suka tattara a lokacin faruwar lamarin a filin wasa na Sao Paulo da ke brazil.
Bayan matakin dakatar da wasan dai babu bayani kan ranar da za a gudanar da shi har zuwa yanzu.
Bisa ga dokokin Brazil din, duk matafiyin da ya shiga kasar daga birtaniya dole ya killace kansa na kwanaki 14, wanda kuma bayanani ke cewa wasu ‘yan wasan Argentina da ba a bayyana sunansu ba sun ki mutunta tsarin.
Yanzu haka Brazil na jiran haduwarta da Bolivia ne ranar juma’ar nan 10 ga watan Satumba duk dai a wasannin na neman gurbin shiga gasar cin kofin Duniya.