Hukumar FIFA ta sanar da yiwuwar baiwa kasashen Brazil da Argentina damar doka wasansu na neman gurbin zuwa gasar cin kofin duniya da ta dakatar a bara sakamakon takaddama kan karya dokokin yaki da covid-19 da ya kai ga rikici.
Duk da cewa kasashen 2 dukkaninsu sun samu tikitin zuwa gasar ta cin kofin duniya da za ta gudana a Qatar a karshen shekarar nan, amma dukkaninsu sun suna bukatar doka wasan cikin takardun da suka aikewa FIFA.
A baya dai FIFA ta yi watsi da daukaka karar da kasashen 2 suka shigar don basu damar doka wasan da kuma janye tarar da aka lafta musu saboda takaddamar ta ranar 5 ga watan Satumban bara, wanda ya kai ga basu damar doka wasan a watan Fabarairu amma karkashin tsauraran sharudda da dukkaninsu suka ki amincewa.
An dai dakatar da wasan ne a wancan lokaci sakamakon shigar wasu ‘yan wasan Argentina 5 Brazil ba tare da killace kansu na tsawon kwanaki ba wanda kuma ya sabawa dokokin yaki da covid-19.
A wani labarin na daban mai horar da tawagar kwallon kafar Brazil Adenor Leaonardo Bacchi da aka fi sani da Tite ya sanar da shirin yin murabus bayan kammala gasar cin kofin Duniya da za ta gudana a Qatar.
A wata zantawarsa ta SportTV Titte mai shekaru 60 ya ce zai jagoranci Brazil zuwa Qatar amma da zarar sun dawo aikinsa y agama.
Brazil wadda ta dage kofin Duniya har sau 5 a tarihi a wannan karonma na cikin tawagogin da ake yiwa hasashen yiwuwar su kai labari la’kari da irin rawar da ‘yan wasanta ke takawa a lig lig din Turai.
Cikin kalaman kocin wanda y afara horar da Brazil tun daga shekarar 2016 yana fatan kafa tarihin kawowa kasar kofin duniya na 6.
Brazil dai ta dage kofin duniya ne a shekarun 1958 da 1962 da kuma 1994 kana shekarar 2002, kuma tun daga wancan lokaci ne ta fara fuskantar koma baya a fagen tamaula gabanin zuwansa a 2016 da ya dawo da martabar kasar har ta iya kaiwa wasan gab da na karshe a Rasha yayin gasar cin kofin duniya na 2018 gabanin rashin nasara hannun Belgium da kwallo 2 da 1 wanda ek da nasaba da raunin tauraron kasar wato Neymar Junior.