Sir Alex Ferguson ya caccaki matakin kocin Manchester United Ole Gunnar Solsjaer na rashin fara wasa Cristiano Ronaldo a karshen makon da ya gabata.
A cikin minti na 57 ne aka sanya Ronaldo a wasan da Machester ta fafata da Everton a ranar Asabar da aka tashi kunnen doki 1-1.
Ferguson, wanda shine kocin da ya fi samun nasarori a tarihin Manchester United, kamata ya yi kowane mai horarwa ya fara wasa da manyan ‘yan wasansa, yana mai cewa abin da ya fado mai zuciya kenan a lokacin da ya fahimci ba a fara wasan da Ronaldo ba.
Wannan tsokaci na Ferguson zai ta’azzara matsin lamba a kan Solksjaer, duba da cewa ana ganin tsohon kocin na Manchester da kima.
A wani labarin na daban tawagar kwallon kafa ta Young Boys ta yi nasarar lallasa Manchester United duk da kwallo guda da Cristiano Ronaldo ya zura mintuna 13 da fara wasa.
Sauyin da Ole Gunnar Solskjear ya yi a minti na 95 ta hanyar cire Cristiano Ronaldo da Bruno Farnandes ya baiwa Young Boys damar zura kwallonta na biyu ta hannun Jordan Siebatcheu bayan kuskuren Jesse Lingard da ya maye gurbin Ronaldo.
Wasan na jiya shi ne irinsa na 177 da Ronaldo ya buga karkashin gasar ta cin kofin zakarun Turai.
Bugu da kari kwallon Ronaldo mai shekaru 36 ita ce ta 3 da ya zurawa sabuwar kungiyar tasa tun baya kulla kwantiragi da ita a watan jiya.
Wasa na gaba da United za ta doka shi ne tsakanin ta da Villarreal ranar 29 ga watan nan.
A wasannin na jiya dai karkashin rukunin na F Villarreal ta yi canjaras ne da Atalanta da kwallaye 2 da 2 kungiyoyin da dukkaninsu ke dakon haduwarsu da United a nan gaba.