Hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta fitar da wani sabon sakamakon bincike mai shafuka 16 dangane da tallafin kayan aiki da aka bai wa biyu daga cikin ‘yan Saudiyyan da suka kai hare-haren ranar 11 ga Satumban shekarar 2001.
Sakamakon binciken da FBI ta fitar da yammacin ranar Asabar, ya bayyana yadda maharan suka samu taimako daga abokansu aikin sa ‘yan Saudiya da ke Amurka, sai dai babu wata shaida da ke nuna cewa gwamnatin kasar Saudiyya na da hannu a cikin shirin.
Wannan dai shi ne kashin binciken sirri na farko kan hare-haren na 9/11 da hukumar FBI ta fitar tun lokacin da Shugaban Amurka Joe Biden ya ba da umarnin sakin bayanan da suka shafe shekaru ba tare da jama’a sun san su ba.
A makwannin da ya suka gaba Biden ya fuskanci matsin lamba daga dangin wadanda hare-haren na 9/11 suka rutsa da su, wadanda suka dade suna neman bayanan binciken da aka yi bisa azargin cewa manyan jami’an Saudiyya na da hannu a hare -haren.
Zargin hannun
Saudiya a hare-haren na shekarar 2001 ya yi karfi ne lokacin da aka bayyana cewa 15 daga cikin maharan 19 ‘yan Saudiyya ne, zalika Osama bin Laden, shugaban al-Qa’ida na lokacin, shi ma ya fito daga wani babban dangi a kasar.