Wata baturiya ‘yar asalin kasar amurka wacce fasinja ce, ta yada zango a birnin Tehran na Iran a hanyar ta ra zuwa birnin najaf inda zaka shiga sahun masu ziyarar tattakin arba’in na Imam Hussain (S.a), ta bayyana cewa tun da take bata san wata kasa ta ta kai jamhuriyar musulunci ta Iran zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Baturiyar ta bayyana cewa lokacin da zata baro kasar ta ta amurka, mutane suna ganin kamar wani abu ne da bazai yiwu ba ace zata taho tattakin kuma wai har zata bi ta kasar Iran, tace amma bata saurari zantukan mutane ba haka ta biyo jirgin fasinja ta tafi tattakin yanzu kuma ga ta a cikin jamhuriyar musulunci ta Iran kuma ta ga abinda ya bata mamaki dangane da yadda ta samu kasar cikin zaman lafiya da kwanciyar hankali gami da son baki da mutunta mutane.
A tambayoyin da ‘yan jarida suka mata matar ta bayyana cewa ta samu sha’awar ta ziyarci Imam Hussain (S.a) domin ta san wanene shi, me yayi kuma ta yanzke shawarar bi ta Iran ne domin ta san abubuwa da dama wadanda da ake bata labari.
Matar ta kada baki tace bata damu da rahotannin da kafafen yada labari irin su BBC da CNN ke yadawa dangane da jamhuriyar musulunci ta Iran ba domin ita yanzu ta ga tabbas da idanun ta kuma ta tabbatar wadancan kafafen yada labaran suna tsoratar da al’umma ne kawai dangane da Iran.
Tace lokacin suna tattaunawa da mahaifin ta ita kanta abin yana bata tsoro sakamakon yadda kafafen yada labaran yammacin turai ke bayyana Iran din amma yanzu da ta samu kanta a Iran ta tabbatar da samun aminci kuma tana ganin babu wani waje da ya dace mutum yaje domin bude ido wanda ya kai jamhuriyar musulunci ta Iran.
Kuna iya kallon wannan fasinja a manhajar tuwita idan kuka bi wannan mannau din;Twitter Tattaki Arba’in