Fashewar bam a masallaci a kasar Afghanistan yayi sanadiyyar mutuwar masallata 12 kamar yadda jami’an ‘yan sanda suka bayyana, wanda hakan ya kawo karshen kwanaki ukun da kungiyar Taliban ta bayar na tsagaita wuta don bukukuwan sallah karama.
Cikin mutane biyun da suka mutu har da limamin masallacin, a yayin da 15 suka jikkata.
Da take jawabi jami’ar yada labaran rundunar ‘yan sandan yankin Shakar Darah, Ferdaws Framurz ta ce ‘yan ta’addan sun kai harin bam ne cikin masllacin a daidai lokacin da ake tsaka da sallah.
Wannan hari dai shine na farko tun bayan da Mayakan Taliban suka bada sanarwar tagaita wuta ta kwanaki Uku saboda bai wa jama’a damar gudanar da bukukuwan Sallah karama cikin kwanciyar hankali.
Dama dai kasar Afghanistan ta dade tana fama da rashin tsaro, amma fashewar bama baman ya kara tsananta ne bayan da Amurka ta fara janye dakarun ta daga kasar tun ranar daya ga watan da muke ciki.
Hukumomin Afghanistan sun ce adadin wadanda suka mutu, yayin sakamakon fashewar wani bam kusa da wata makarantar mata dake yammacin Kabul ya kai 50, da dama kuma sun jikkata, a yayin da kungiyar Taliban ke ci gaba da musanta hannu a aika aikar.
A yau Lahadi mutane da dama ke binne ‘yan uwansu da lamarin ya rutsa da su a wani wuri da ake wa lakabi da ‘makarbarta masu shahadu’
Ana zargin da hannun amurka a harin bama baman da ake kaiwa baya bayan nan a kasar ta afganistan.
Tun dai dai da amurka ta ayyanan aniyar ta na ficewa daga kasar bayan yakin shekaru sama da ashirin da tayi a kasar aka fara shaidar sabbin fashewar bama bama wanda ake zargin da sanya hannun amurkawan a fasheawar bama baman.