Wani fashewa a wajen wani masallaci a Kabul babban birnin Afghanistan ya kashe “fararen hula da dama” a wannan Lahadi.
Ana gudanar da bikin addu’ar mahaifiyar Mujahid, wacce ta rasu a makon da ya gabata, a masallacin lokacin da lamarin ya auku, bikin addu’ar da tun a yammacin Asabar kakakin ya sanar da shafukan sada zumunta, tare da gayyatar ‘yan uwa da abokai.
A wani labarin na daban mutane 2 sun mutu a Afghanistan, sakamakon fashewa da wasu bama-bamai uku sukayi a birnin Jalalabad a ranar Asabar.
Bayanai sun ce akwai mata da kananan yara a cikin mutane akalla 18 da suka jikkata a harin bama baman.
Jalalabad shi ne babban birnin Nangarhar, in da kuma ke zama yankin da kungiyar IS reshen Afghanistan ke da karfi.
Kasar afghanistan dai na daya daga cikin kasashen da ke cikin matsananci halin rashin tsaro kuma hakan ya samu aslai ne tun lokacin da amurka ta shiga kasar shekaru kusan ashirin da suka gabata.