Fashe fashe uku a yankin ‘yan Shi’a na birnin Kabul; Dalibai 26 ne suka yi shahada.
Wani harin bam da aka kai a wata makaranta da ke yammacin birnin Kabul ya kashe mutane akalla biyu tare da jikkata wasu da dama; Wasu rahotanni sun ce sama da dalibai 20 ne suka mutu sakamakon tashin bama-baman.
Fashewar farko ta afku ne a cibiyar ilimi ta Mumtaz sai kuma na biyu a babbar makarantar Abdul Rahim Shahid.
Fashewar da aka yi a makarantar sakandare ta Abdul Rahim Shahid ta faru ne a daidai lokacin da daliban suka yi ta kara suka fice daga ajujuwa, sai kuma bam na biyu a lokacin da suke taimakon wadanda suka jikkata.
Wasu rahotanni na nuni da cewa dalibai 26 ne suka yi shahada a tashin bam din
Jim kadan gabanin tashin bama-baman biyu, an sake samun wani tashin bam a wata makarantar firamare da ke yammacin birnin Kabul, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane daya zuwa shida tare da jikkata wasu da dama.
Har yanzu dai babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
READ MORE : Jiragen Yakin HKI Sun Yi Lugudan Wuta A Yankin Khan Yunus Da Sanyin Safiyar Yau.
READ MORE : Kasar Afirca Ta Quds Ta Sanar Da Kafa Dokar Ta Baci Dangane Da Bala’in Dabi’a.