Ya ce matakin janyewar Amurka daga kasar Afghanistan da kuma yadda aka aiwatar da hakan cikin kankanin lokaci ya bai wa kowa mamaki kuma ya rage farin jinin joe biden dina Amurka, duk da cewa Biden ya danganta hakan da matsaloli na tattalin arziki da kuma asarorin da hakan ke jawowa Amurka.
Farfesa Bensel ya ce, abin da yafi dangane da janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan shi ne, yadda suka janye ba tare da sun yi wani shiri na taimaka ma kasar ba domin ta tsaya a kan kafafunta, ta fuskoki na tsaro da tattalin arziki da kuma kyautata rayuwar jama’ar kasar, domin kasantuwar Amurka yasa kasar a cikin manyan kalubale a dukkanin wadannan fuskoki.
Ranar Talata 11 ga Satumban 2001, ne wasu masu alaka da kungiyar al- Ka’ida su 19 suka kwace jiragen sama guda 4 tare da kai hare-haren kunar bakin wake a Amurka kan tagwayen gine gine na Cibiyar kasuwanci ta Duniya da ke birnin New York, da ma’aikatar tsaro ta Pentagon da ke Washington, yayin na fado, a jihar Pennsylvania.
Kusan mutane 3,000 suka mutu yayin harin wanda ya kasance mani muni a tarihin Amurka.
Shugaban Amurka Joe Biden, sabanin shugabanin da suka gabace shi, ya fitar da wani faifan bidiyo maimakon yin jawabi yayin bikin zagayowar ranar inda ya bukaci Amurkawa dasu hada kansu, wanda shi ne karfin kasar inji shi.
Kafin hakan dai, Mista Biden ya ba da umarnin sakin wasu bayanan sirri dangane da binciken gwamnati kan harin na ranar 11 ga watan satumban 2001.