Harin makaman atilare a gabashin Ukraine, da kuma umarnin mayakan ‘yan awaren da ke samun goyon bayan Rasha ga farar hula na ficewa daga yankin, ya sake dagula lamura tare da kara zaman fargabar da ake dangane yiwuwar sojojin Rasha su mamaye kasar ta Ukraine.
Sai dai Amurka ta ce da kimanin sojojin Rasha dubu 149,000 ne ke kusa da iyakokin Ukraine kuma idan aka hada da mayakan ‘yan aware, yawansu zai kai dubu 190,000, matakin da Amurkan ta ce batun musanta shirin kaddamar da yaki ma bai taso ba, sai dai kawai a tantance lokacin da Rashan da kuma magoya bayanta za su afkawa Ukraine.
A baya bayan nan ma’aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa, shugaba Vladimir Putin da kansa zai sa ido a kan atisayen da aka shirya na gwajin makamai masu linzami da za su iya dakon makaman nukiliya a yau Asabar saboda haka babu bukatar fargabar barkewar yaki
Wani wakilin Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP da ke kusa da inda aka kallon kallo tsakanin sojojin gwamnatin Ukraine da kuma yankin mayaka masu goyon bayan Rasha a yankin Lugansk, ya ji karar fashewar wasu abubuwa tare da ganin gine-ginen fararen hula da suka rushe daga cikin iyakar Ukarine.