Farashin gangan danyan man fetur ya kara tashi a kwasuwannin duniya, inda ya kai kusan dala 140 a kan kowacce ganga, sakamakon mamayar da Rasha ta yiwa Ukraine.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ministan kudin Jamus da na harkokin waje ke gargadi akan daukar duk wani mataki na haramta sayen man Rasha.
A ranar Lahadi, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken yace suna duba yiwuwar hana Rasha sayar da man ta a kasuwannin duniya, matakin da Jamus wadda ke shugabancin kungiyar G7 ke cewa bamai dorewa bane, domin kuwa hakan zai hana su samun wutar lantarki a Jamus.
Kasar Jamus na daya daga cikin kasashen da suka dogara da Rasha wajen samun gas da man fetur, inda take sayen kashi 55 na iskar gas daga wurin ta da kuma kashi 42 na man fetur.
A wani labarin na daban Shugaban Kamfanin man fetur na NNPC a Najeriya Mele Kyari ya ce ya dace a dinga sayar da litar mai guda akan sama da naira 280 saboda wahalar da ake yi wajen sarrafa shi da kuma samar da shi ga jama’a.
Shugaban kamfanin NNPC ya ce babu wata kasa a duniya da ta ke sayar da man dizil da manyan motoci da injina ke amfani shi fiye da farashin man fetur kamar yadda ake yi yanzu a Najeriya inda ake sayar da lita guda na dizil akan naira 280, yayin da kuma ake sayar da fetur akan naira 162.
Kyari yace shugaban kasa Muhammadu Buhari ya basu umurnin daukar matakan da suka dace na tabbatar da cewar ba’a kara farashin man yadda zai gagari talakawa ba musamman a wannan lokaci.
Jami’in ya ce wannan umurni ya nuna cewar za su dinga amfani da wasu kudaden da ya dace a yiwa jama’a aiki da su wajen sanya tallafin da gwamnati ke zubawa domin daidaita farashin man.
Shugaban kamfanin da yace babu wata alama na kara farashin man a watan Yuli mai kamawa yayi zargin cewar fasa kwabrin man da ake yiwa zuwa kasashen makota na daga cikin dalilan dake nuna yawan man da ake amfani da shi a cikin gida.