Farashin danyen man fetur yana ci gaba da kara hauhawa a kasuwanninsa na duniya, inda mai na “Brent” farashinsa ya haura dalar Amurka 101 a kowace ganga a yau Laraba, wanda shi ne karon farko tun daga ranar 3 ga wannan wata na Agusta.
Da karfe 11:50 na safiyar yau agogon Moscow, farashin danyen mai na Amurka “West Texas Intermediate” ya tashi da kashi 1.28% zuwa $94.94 a kowace ganga daya, yayin da kuma farashin danyen mai na Brent ya tashi da kashi 1.32% zuwa dala 101.4, a cewar kafar yada labarai ta Bloomberg.
Tashin farashin dai ya biyo bayan rahotannin da kafofin yada labarai suka bayar, da ke cewa majiyoyin kungiyar ta OPEC +, wadda kungiyar da ta hada da Rasha da Saudiyya, na iya matsawa wajen rage yawan man da ake hakowa a kowace rana, idan aka samu cikas bayan cimma yarjejeniya tsakanin Iran da kasashen yammacin Turai kan yarjejeniyar nukiliya, da kuma dage takunkumin da aka kakabawa kasar ta Iran.
A wani labarin na daban rundunar sojojin Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta fara wani gagarumin atisaye na sarrafa jirage marasa matuki da aka kera su da fasaha ta musamman ta zamani, domin kai hare-hare da kuma gudanar da ayyuka na leken asiri.
Wannan atisayen dai ana gudanar ad shia dukkanin bangarori na kasar Iran, daga gabashin kasar har zuwa yammaci, daga kudanci har zuwa arewaci da kuma cikin tekun fasha.
Admiral Seyyed Mahmoud Mousavi, mataimakin babban kwamandan rundunar sojin kasar Iran, kuma mai magana da yawun atisayen na hadin gwiwa a tsakanin dukkanin bangarorin soji na sama da kasa da ruwa, ya bayyana cewa atisayin shi ne irinsa na farko da sojojin Iran suke gudanarwa da ake amfani da jiragen yaki marasa matuki zalla.
Ya kara da cewa, a cikin wannan atisayin ana gwada sabbin jiragen yakin marasa matuki da Iran ta kera, wadanda za su iya daukar makamai masu linzami da kuma kai hari da su daga tazara mai nisan gaske a cikin sararin samaniya.
Ya ce wannan yana zuwa ne domin kara zama cikin shirin ko ta kwana domin fuskantar kowace irin barazana a kan kasar, da kuma mayar da martanin da ya dace a nan take.
Source: LEGITHAUSA