Farashin Danyen Mai Ya Kai Dala 120 Bayan Harin Da Akai A Matatar Aramco.
Majiyar labarai daga kasar Saudiya sun bayyana cewa An ga hayaki ya turnuke asararin samaniya sakamakon gobar da ta tashi na harin ramuwar gayya da dakarun sojin kasar Yamen suka kai a kasar Saudiya dake birnin Jidda.
A jiya juma’a ce dakarun sojin kasar Yamen suka kai hari kan kayan aiki na matatar mai na Aramco dake birnin Jidda dake kasar Saudiya . rahotomn ya nuna cewa harin ya kawo cikas a tsarin wutar lantarki da hakan ya jawo ayyuka suka tsaya cak a kamfani .
A wani bayani da dakarun kasar ta Yamen suka fitar sun nuna cewa harin nasu somi tabi ne, za su ci gaba da kai hare-hare a kasar ta Saudiya har sai an cire takunkumin da aka kakabawa kasar.
READ MORE : A Yau Ce Jam’iyyar APC Mai Mulki A Najeriya Take Gudanar Da Babban Taronta Na Kasa.
Dubban mutane ne aka kashe wasu aka jikkata su , tare da tialastawa miliyoyi yin gudun hijra daga lokacin da kasar Saudiya ta kaddamar da harin soji a kasar Yamen zuwa yanzu. Tare da rusa kashi 85 cikin dari na muhimman gine-ginen kasar.
READ MORE : Najeriya; Jam’iyyar APC Ta Zabi Sanata Abdullahi Adamu A Matsayin Sabon Shugabanta.