Jawabin Macron ya biyo bayan tattaunawar da aka shafe watanni ana yi tsakanin masu ruwa da tsaki kan aikin ‘yan sanda da kuma dangantakar su da jama’a, biyo bayan bidiyon da ke nuna wasu ‘yan sanda fararen fata 4 suna lakadawa wani bakar fata dukan kawo wuka a dakinsa na shirya wakoki da ke birnin Paris a watan Nuwamban shekarar bara.
Cin zarafin da aka yi wa Michel Zecler ya fusata jama’a, ciki har da masu fafutukar kare hakkin dan adam na Black Lives Matter da ke Faransa, wadanda suka yi A-wadai da munanan dabarun da ‘yan sanda ke amfani da su kan marasa rinjaye, musamman maza bakar fata da Larabawa.
Daya daga cikin jerin soke-soken da aikin ‘yan sanda ya dade yana fuskanta a Faransa, shi ne rashin wanzuwar wata hukuma mai zaman kanta da ke sa ido kan ake aiwatar da shi.
Hukumar IGPN wato “Inspection Generale de la Police Nationale, da a halin yanzu ke sauraron korafe -korafe, yawancin jami’an ta ‘yan sanda ne kuma ministan cikin gida, ke nada wanda zai jagorance ta.