Masu zanga zanga sun mamaye titi a babban birinin Faransa watau Paris, hakan ya biyo bayan wani da wariyar launin fata da ya bindige mutane har uku zuwa lahira kuma ya jinyata da dama.
Harin wanda aka kai a matattarar al’adu ta “Kurdawa” ya sanya birnin na Paris din cikin halin rashin tabbas wanda wanda ya sanya dole ministan cikin gida ya bayyana a wajen da lamarin ya faru.
”Mutum uku ne suka mutu, daya yana bangaren kulawa ta musamman a dai dai lokacin da biyu kr cikin mawuyacin hali, wanda ake zargi shima daaka kama shi yaji rauni a fuska” Kamar yadda maigabatar da kara na Faransa ya sanar da manema labarai a ranar juma’a.
A kusa da inda wannan lamari ya faru kuma mambobin “Kurdawan” Faransa suka shiga zanga zanga wacce ta sanya suka fuskanci fushin ‘yan sanda, wadanda suka dingi harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa fusatattun masu zanga zangar.
A wasu rahotanni an tabbatar da cewa, sakamakon jefa ababen jefawa kan ‘yan sandan da aka dingi yi har an lalata mota.
Amma sai dai mai gabatar da karar na Faransa ya tabbatar da cewa wanda ake zargin dan shekara 69 an sha kama shi da laifuka masu alaka da wariyar launin fata.
Amma har yanzu masu bincike basu iya kaiwa ga tabbatar da dalilin wanda ake zargin na kai wannan hari a matatatrar al’adu ta kurdawan da kuma wani shago gami da wani shagon aski ba.
“AFP News” ta tabbatar da cewa, wasu shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa sun ji karar harsashi har takwas da kunnuwan su.
Shaidun gani da idon sun bayyanawa “AFP News” cewa tsohon wanda ‘yan sanda suka bayyana farar fata ne ya fara da kai hari matattarar kurdwan kafin ya shiga shagon askin inda aka kama shi.
Wannan ba shine karona farko da ake samun tarzoma a birnin Paris ba a baya bayan nan.