Faransa; Yan Majalisar Dokoki Da Dama Sun Ya Yi Allwadai Da Tsarin Wariya Na Isra’ila A Falasdinu Da Ta.
Yan majalisar dokokin kasar Faransa kimani 38 suka rattaba hannu kan wani kuduri a majalisar wanda yayi allawadai da tsarin wariyar da gwamnatin haramtacciyar kasar Isara’ila take aiwatarwa a kasar Falasdinu da ta mamaye.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto cewa wani dan majalisa mai suna Jean-Paul Lecocq ne ya gabatar da kudirin a majalisar dokokin kasar ta Faransa, wanda kuma ya jawo cecekuce a ranar jumma’a 13 ga watan yulin da mujke ciki a tsakanin mutanen kasar. Amma daga baya dai fitattun yan majalisar daga jam’iyyar NUPES masu adawa don rattaba hannu kan kudurin.
Daga cikin wadanda suka sanya hannuj kan wannan kudurin dai akwai Fabien Roussel, yan majalisu daga jam’iyyar “France Proud” kamar Adrien Katniss, comred Christine Pierce-Bonn, da both Aurelian Tashi da kuma Sabrina Sabaihi na jam’iyyar ‘Green Party’.
READ MORE : MDD Ta Bukaci Masana Su Samar Da Sabbin Alluran Riga Kafin Cutar Covid 19.
Tun shekara ta 1948 ne yahudawan Sahyoniya suka kafa kasar Israel kan kasar Falasdinu sanna suka ci gaba da gallazawa mutanen kasar wadanda basu gudu suka bar kasan ba. Kuma sun aiwatar da kashe kashin kiyahsi kan al-ummar Falasdini don bukatar uahudawan.