Faransa ta yi bikin cika shekaru 60 da rattaba hannu kan yarjejeniyar Evian – wanda ya kawo karshen yakin Aljeriya tare da share fagen samun ‘yancin kai daga Faransa – a wani biki da aka gudanar a fadar Elysée.
Wato duk da irin barnar da yakin neman yancin kai na shekaru takwas ya haifar a karshe ya kawo karshe bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar Evian a ranar 18 ga Maris, na shekarar 1962.
Masana tarihi na Faransa sun ce fararen hula da mayaƙa rabin miliyan ne suka mutu – 400,000 daga cikinsu ‘yan Algeria ne – yayin da hukumomin Algeria suka yi imanin an kashe kusan myane miliyan 1.5.
A karkashin Janar Charles de Gaulle na Faransa, wanda gwamnatinsa ta sanya hannu kan yarjejeniyar, da kuma magajinsa Georges Pompidou, Paris na da kyakkyawar alaka da Algiers. Haka abin yake a lokacin François Mitterrand, duk da cewa ya kasance ministan harkokin cikin gida lokacin da Aljeriya ta fara gwagwarmayar ‘yancin kai a shekarar 1954 kuma ya kasance mai adawa da ‘yancin kan kasar.
A wani labarin na daban Ukraine ta yi kira ga China da ta fito ta caccaki matakin da Rasha ke dauka a kanta kamar yadda sauran kasashen yamma suka yi, bayan da Amurka ta gargadi Chinar a game da sakamakon bada goyon baya ga Rasha.
Wannan na zuwa ne bayan da Rasha ta fito ta ce ta yi amfani da wani shu’umin makami mai linzami, wanda gudunsa na ninka na sauti har sau 10 wajen lalata rumbunan ajiyar makaman Ukraine a yammacin kasar.
A wani jawabi na kai tsaye, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya caccaki kamfanoni ciki har da Nestle sakamakon ci gaba da mu’ammalar kasuwanci da suke yi da Rasha duk da yadda yara kanana ke mutuwa a kasarsa.