Mahukunta a Faransa sun tura karin jami’an tsaro zuwa yankin Guadelouope, bayan da aka share tsawon kwanaki ana tarzoma tare da kone-kone don nuna rashin amincewa da sabbin matakan hana yaduwar cutar Covid-19.
Ina godiya ga mazauna yankin Guadeloupe wadanda suka amince aka yi masu allurar kariya, domin idan aka yi la’akari da adadin wadanda suka karbi allurar, hakan na nuni da cewa mutane kalilan ne ke adaewa da matakan muke dauka. inji Macron.
Shugaban na faransa ya kara da cewa “mazauna yankin Guadeloupe, da yankin Martinique har ma da Guiana maza da mata duk sun fahinci cewa yin allurar abu ne da ya dace.”
Macron ya ce, ba za su taba yin wasa da duk wani lamari da ya shafi kare lafiyar Faransawa ba don cimma muradunsu, yana mai cewa, za su ci gaba amfani da hanyoyin lalama don kwantar da hankulan jama’a.
A wani labarin na daban kuma shugaban Faransa Emmanuel Macron ya dage cewa ba zai “yi watsi da bukatun” masuntar kasar da ke neman lasisin kamun kifi a tsibirin Channel na Jersey, kamar yadda yarjejeniyar bayan Brexit ta tanadar, lamarin da ke haifar da munanan kalamai tsakanin kasashen biyu dake neman rikidewa zuwa yakin kasuwanci.
Yayin wata ziyara da ya kai arewacin kasar ranar Jumma’a shugaba Macron yace za su ci gaba da fafutuka, ba tare da yin kasa a guiwa ba kan bukutun masuntan kasar.
Macron ya yi kira ga Hukumar Tarayyar Turai da ta kara zage damtse wajen tursasawa Jersey, dake karkashin Birtaniyya, don girmama sharuddan yarjejeniyar kasuwanci da kungiyar bayan ficewar Birtaniya daga cikin gungun Turai.
Faransa dai na cikin kasashen da suke kokarin yima mutanen su rigakafin cutar korona ko da ba bisa amincewar su bane.