Ministar Tsaron Faransa Florence Parley ta ce Girka ta amince da sayen karin jiragen yakin da suke kerawa kirar Rafale guda 6.
Girka ce dai kasar Turai ta farko da ta sayi jiragen yakin na Rafale daga Faransa, inda a watan Janairun da ya gabata, ta biya euro biliyan 2 da miliyan 500 akan jiragen guda 18, da zummar inganta karfin sojinta, sakamakon zaman tankiyar da ke tsakaninta da Turkiya.
A watan Mayu, Croatia ta zama kasa ta biyu ta Turai da ta sayi Rafales, inda ta zabi jirage 12 da aka yi amfani da su a baya.
Fira Ministan Girka Kyriakos Mitsotakis yace gwamnatinsa za ta sayi makamai masu yawan gaske gami da yiwa rundunar sojin kasar garambawul, a daida lokacin da zaman tankiya ke karuwa tsakanin kasar ta Girka da Turkiya a gabashin Meditaraniya.
Wani lokaci a yau lahadi ake sa ran Fira Ministan Girka zai yi karin bayani kan wannan shiri, da ya cimma aiwatarwa bayan ganawarsa da shugaban Faransa Emmanuel Macron, kan takaddamar da ta kunno kai tsakaninsu da Turkiya kan arzikin mai da iskar gas dake iyakokinsa a gabashin tekun Meditaraniya.
A bangaren Turkiya kuwa, a karshen makon nan shugaba Recep Tayyib Erdogan ya gargadi Faransa da cewar za ta dandana kudarta, muddin ta cigaba da yin katsalandan a rikicin arzikin kan iyakar dake tsakaninta da kasashen Girka da kuma Cyprus.