A wannan Asabar Faransa ta karrama Samuel Paty, malamin makarantar da aka fille wa kai shekara daya da ta gabata, bayan nuna wa dalibansa hotunan zanen batanci na annabi Muhammad wanda Tsira da Amincin Allah suka tabbata gare shi.
Mutuwar Paty, tayi matukar girgiza Faransawa musamman masu goyon bayan batanci ga annabi muhammadu (s.a.w.w) da wasu daga cikin masu aikin koyarwa da ke cewa kisan ya yi hannun riga da martabar aikin koyarwa da bai kamata a cusa batun addini a cikin sa ba, bai kima kamata abi kadin koyarda kiyayyar annabin musulunci da samuel paty keyi a makarantara sa ba.
Firaministan Faransa Jean Castex, wanda ke gabatar da jawabi dangane da cika shekara daya da faruwar kisan, ya ce shirya bikin girmamawa ga Samuel Paty tamkar girmama ce ga kasa kasa baki daya.
An dai gudanar da wannan biki ne a gaban manyan jami’an gwamnati da suka hada da ministan ilimi Jean-Michel Blanquer, sai dangi da kuma makusantan marigayi Paty.
A wani labarin na daban wasu kasashen larabawa sun amsa kiran shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan da wasu kasashen musulmi wajen soma kauracewa kayakin Faransa, biyo bayan kalaman Shugaban Faransa Emmanuel Macron dake tamkar batanci ga addinin musulunci.
Shugaba Macron ya bayyana hakan ne dangane da kisan da aka yiwa mallami tarihin nan, da masu ikirarin jihadi da karfin tsiya suka hallaka kwanakin baya, sakamakon nunawa daliban sa zanen batanci ga manzon tsira Annabi Mohammadu tsiri da amincin Allah su tabbata a gareshi.
Matakin da ya harzuka wasu kasashen musulmi da yanzu haka suka sanar da dakatar da saya ko amfani da kayakin da aka sarrafa a Faransa ko ke dauke da sunan kasar.
Ranar juma’a 23 ga wannan wata na Oktoba ne kasar Koweit ta shiga sahun gaba daga cikin masu adawa da takawa kayakin Faransa birki a kasarta, lamrain da ya dada yaduwa a sassan wasu kasashen larabawa.
Wasu daga cikin manyan masana’antun Faransa dake sarrafa kayaki da ake shiga da su kasashen Larabawa sun hada da Kiri, da Babybel da suka shafi sashen sufuri sun bayyana damuwa matuka.
Qatar da Koweith da Pakistan na daga cikin jerryn kasashen da suka kauracewa amfani da kayakin Faransa, biyo bayan kalaman Shugaba Emmanuel Macron tun bayan kisan Samuel Patty, sai dai rahotanni daga Masar da Iran da Irak dama Turkiya kamar dai yada wakilan Rfi suka tabbatar ,jama’a basu soma nuna kyamar kayakin Faransa a can ba.