Kasar faransa a ranar juma’ar da ta gabata ta sanar da janye huldar diflomasiyya gami da janye jakadun ta dake kasashen amurka da australiya sakamakon abinda ta kira da yankan baya kuma wanda ka iya samar da matsala mai dorewa a yanzu da kuma zuwa gaba a nahiyar turai.
Makasudin faransa na janye jakadun nata dai baya rasa nasaba da wani kwantaragi wanda ya kai na a kalla dalar amurka miliyan dari hudu, wanda faransan ta rasa kuma amurka ta amshe wannan kwantaragi.
Ranar alhamis ne dai ministan harkokin wajen faransa ya kira wannan kwantaragi da yankan baya, inda takwaran sa na kasar sin watau chana ya bayyana wannan kwantaragi a matsayin babban dalilin da zai kawo nakasu a zaman lafiyar yankin turai kuma zai bada yanayin ‘yar tsere wajen mallakar makamai tsakanin kasashen nahiyar.
Bincike ya tabbatar da cewa harkar sayar da makamai ga gwamnatocin kasashe na cikin manyan hanyoyin da kasashen turai ke samun kudin shiga, sai dai ta bangare guda hakan na zaman babbar barazana ga zaman lafiyar duniya domin makaman da kasashen turan ke kerawa akasari ana kashe al’ummomin da basu ji ba basu gani bane dasu.
Ko a kwanakin baya ma dai kasar amurkan ta shiga wani kwantaragi na sayarwa da kasar saudiyya jiragen yaki wadanda kudin su ya kai dalar amurka miliyan dari hudu.
Saudiyyar da ke kashe fararen hula ba dare babu rana a kasar yemen amma amurka na shirye ta saida mata da makaman yaki.
Idan ba’a mance ba dai saudiyya ce ta kashe shahararren dan jaridar nan jamal kashshogi, wanda masarautar saudiyyan bata jima da neman afuwa dangane da waccan ta’asa da ta aikata ba.
Kari a kan hakan bincike ya tabbatar da cewa gwamnatin saudiyyar ce dai ta dauki nauyin kisan kiyashin zariya na sha biyu ga disambar 2015 wanda aka kashe ‘yan najeriya fiye da dubu a kasa da kwana ukku.