Hukumomin Faransa sun ci tarar babban kamfanin sadarwa na Google Euro miliyan 220 bayan sun zarge shi da watsa tallace-tallace a shafin intanet domin fifita kansa tare da yi wa aboban gogayyarsa zagon-kasa.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanin na Google ke ci gaba da fuskantar matsin lamba a nahiyar Turai.
Tarar wani bangare ne na jituwar da aka cimma, bayan wasu kafafen yada labarai uku na Turai da suka hada da News Corp da Le Figaro da Groupe Rossel sun zargi Google a 2019 da wuce-gona-da-iri wajen yin kane-kane a kasuwar intanet ta hanyar mamaye tallace-tallace.
Hukumar da ke sanya ido kan gogayyar kasuwanci a Faransa ta ce Google na fifita tallace-tallacensa tare da yin amfani da wasu dabaru na janyo hankulan kwastamomi don latsa tallace-tallacen nasa.
Kafafen yada labarai da ke neman kafar sayar da gurbin talla a shafukansu na intanet ko kuma manhajojinsu na kan wayar salula, sun fahimci cewa, Google na yi musu zagon-kasa domin kuwa shi ma yana gogayya da su a shafin na intanet.
Daga cikin abubuwan da Google din ke yi har da kankance tallace-tallacen takwarorinsa tare da bai wa kwastamomi wahala wajen latsa tallace-tallancesu, amma kuwa ba ya yi kansa haka.
Hukumomin da ke sanya ido kan gogayyar kasuwanci a Faransa sun ce, Google na nuna wannan halayyar ne domin danne sauran masu fafatawa da shi a fagen kasuwancin intanet.
Manhajar ta google ta shahara danne hakkin wadanda suka saba mata a fannoni da dama wanda hakan yake jawo cece-kuce daga lokaci zuwa lokaci idan suka danne hakkin wasu.
Kamfanin google sun shahara a wannan ta’ada musamman idan lamarin ya hada da musulmi.