Kasar Faransa ta ce yana da matukar muhimmanci a kammala tattaunawar da wakilan kasashen duniya ke yi wajen cimma matsaya kan farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran a wannan mako.
Kasashen dake cikin yarjejeniyar ta shekarar 2015 na kallon wannan yunkuri a matsayin hanyar da ta rage na hana kasar Iran gina makamin nukiliya zargin da kasar ke ci gaba da musantawa.
Yanzu haka babban jami’in dake wakiltar Iran wajen tattaunawar Ali Bagheri ya koma Vienna daga Tehran inda yaje tuntuba domin ci gaba da shiga taron.
Kasashen dake cikin tattaunawar sun hada da Faransa da Jamus da Birtaniya da Rasha da China da kuma Amurka bayan ita Iran.
Yarjejeniyar ta shekarar 2015 ta cirewa Iran takunkumin karya tattalin arzikin da aka kakaba mata saboda shirin nukiliyar, amma sai kasar Amurka tayi gaban kan ta wajen janyewa daga cikin ta a shekarar 2018 lokacin jagorancin shugaba Donald Trump wanda ya sake sanyawa Iran sabbin takunkumin karya tattalin arziki.
Wannan mataki na Trump ya sa Iran ta koma ci gaba da shirin tace sinadarin uranium da ake zargin zata gina makamin da shi.
Yayin gudanar da wannan taro na Vienna Iran tayi ta bukatar bata tabbacin cewar gwamnatin Joe Biden ba zata dauki irin matakin da Donald Trump da ya gada ta dauka ba.
A wani labarin na daban Matakan da kasar Amurka ta dauka na cire wasu jerin takunkuman karayar tattalin ariziki da ta saka kan kasar Iran abu ne mai kyau, sai dai ba su wadatarwa, in ji ministan harakokin wajen Iran. Bayan da Amurka ta bayyana soke wasu jerin takunkumai da ta saka wa kasar, da ke da alaka da aikin samar da makamashin nukliyar da kasar ta Iran ke yi.
Matakin da gwamnatin Joe Biden ta dauka ya kasance mai mahimmanci ga mahukumtan Téhéran a dai dai wannan lokaci da a birnin Vienne, a ke ci gaba da tattaunawar yinkurin ceto yarjejeniyar 2015 kan aikin Nukliyar da ke kan ganiyar karshe.
A 2018 ne, shugaban Amruka da ya gabata Donald Trump, ya janye kasarsa daga cikin yarjejeniyar tare da maida daukacin takunkuman kariyar tattalin arizikin da Amrukar ta kakabawa kasar ta Iran, al’amarin da ya sa, Iran jingene aiki da wasu fannoni na yarjejeniyar kawo yanzu da gwamnatin shugaba Biden, ta sake maido kasar kan teburin tattaunawar neman ceto tsohuwar yarjejeniyar ta 2015 amma tare da kwaskwarima. Matakin da Iran ta ce ba ta yarda da shi ba.