Faransa; Macron Da Le Pen Za Su Je Zagaye Na Biyu A Zaben Shugaban Kasa.
Bayan gudanar da zaben shugaban kasa a Faransa a jiya Lahadi, sakamakon zaben ya nuna cewa, Macron ya samu kashi 27.7%, yayin da Le Pen ta zo ta biyu da kashi 23.%.
A bisa tsarin zaben kasar Shugaban Emmanuel Macron zai fafata da Marine Le Pen a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar saboda gazawa wajen samun isassun kuri’un da zasu bashi nasara ba tare da zuwa gagaye na biyu ba.
Dantakara Jean-Luc Melencheon ya zo na uku da kusan kashi 22% cikin dari na dukaknin kuri’un da aka kada a tsakanin ‘yan takara goma sha biyu da suka kara a zaben, wanda hakan ke nufin an yi waje da shi.
A bisa bayanin da Hukumomin kasar ta Faransa suka fitar, kashi 65% na masu kada kuri’u ne suka fito domin kada kuriunsu a jiya a zaben na shugaban kasa.
Tuni dai wasu daga cikin ‘yan takarar da suka sha kashi suka fito suka nuna goyon bayansu ga daya daga cikin ‘yan takarar biyu da za su kara a zagaye na biyu, yayin da kuma har yanzu wasu daga cikinsu bas u yanke shawara kan hakan ba.