Rahotani daga kasar Syria na cewa, an fara gudanar da tarukan arba’in na Imam Hussain (AS) a hubbaren Sayyida Zainab da ke kudancin birnin Damascus fadar mulkin kasar.
Wadannan taruka za su ci gaba da gudana har zuwa ranar arba’in na Imam Hussain (AS), inda malamai suke gabatar da jawabai kan abin da ya faru da zuriyar manzon Allah (SAW) karkashin jagorancin Imam Hussain (AS) a hannun sarakunan daular Bani Umayya, na cin zarafi da kisan gilla da tozarci.
A wani labarin na daban jaridar Al-nahar ta kasar Aljeriya ta fara bayar da rahoton cewa, tsohon shugaban kasar Aljeriya Abdelaziz Bouteflika ya rasu marecen jiya Juma’a yana da shekaru 84.
Wanann ya zo ne a cikin sanarwar da fadar shugaban kasar ta bayar, ya kuma rasu ne sama da shekaru biyu bayan sauka daga mukaminsa sakamakon matsin lamba daga masu zanga -zanga da sojojin kasar.
Shi ne shugaban kasar Aljeriya na 7 tun bayan samun ‘yancin kan Aljeriya daga Faransa a shekarar 1962, inda ya fara zama ministan harkokin waje na Aljeriya na farko kuma mai fada a ji a kasar.
An haife shi a cikin sheakara ta 1937, kuma a cewar jaridar ta Al-nahar ya kasance mutum ne mai son karatun kur’ani a rayuwarsa, tun daga kuruciyarsa har lokacin da yake shugabancin kasar ta Aljeriya.
Abdelaziz Bouteflika, gogaggen dan gwagwarmayar neman ‘yancin kai na Aljeriya, ya shafe shekaru ashirin yana mulkin kasar da ke Arewacin Afirka kafin ya yi murabus a watan Afrilun shekarar 2019 bayan gagarumin zanga -zangar watsi da shirinsa na neman wa’adi na biyar.
Ba kasafai aka gan tsohon shugaban ba a bainar jama’a ba tun a shekarar 2013 lokacin da ya gamu da mutuwar bangaren jiki.
Bayan murabus din Bouteflika, a wani yunkuri na kawo karshen zanga -zangar neman juyin juya halin siyasa da tattalin arziki, hukumomi sun kaddamar da binciken da ba a saba gani ba kan cin hanci da rashawa, wanda ya kai ga daure wasu manyan jami’ai da dama, ciki har da babban dan uwan Bouteflika kuma mai ba sa shawara.