Jaridar Guardian ta kasar Burtaniya ta bayar da rahoton cewa, ‘yan sanda sun fara gudanar da bincike kan sanya wuta da aka yi a kan wani masallaci na musulmi a daren jiya Asabar a garin Manchester.
Rahoton ya ce an sanya wutar ne da dare bayan da musulmi da suke gudanar da harkokinsu a wurin suka bar wurin, inda aka saka wuta da ta yi sanadin jawo gobara a masallacin.
Kafin zuwan jami’an kwana-kwana, wasu daga cikin jama’ar gari da suke wucewa sun fara kawo dauki domin kashe wutar da ke ci a masallacin.
Musulmin da suke tafiyar da lamurran masallacin sun yi godiya ga jama’ar yankin, kan yadda suka nuna damuwa da abin da ya faru da kuma gudunmawar da suka bayar wajen kashe wutar da ke ci a masallacin, lamarin da a cewarsu ya nuna musulmi da al’ummar yankin suna zaune laffiya ne da girmama juna.
A nasu bangaren ‘yan sanda a birnin na Manchester suna ganin cewa harin yana da alaka ne da wasu masu akidar kiyayya da addinin muslunci, kuma sun sha alwashin bin kadun lamarin domin gano wadanda suke da hannu a cikin lamarin domin su gurfana a gaban kuliya.
Ya ce matakin janyewar Amurka daga kasar Afghanistan da kuma yadda aka aiwatar da hakan cikin kankanin lokaci ya baiawa kowa mamaki a Amurka, duk da cewa Biden ya danganta hakan da matsaloli na tattalin arziki da kuma asarorin da hakan ke jawowa Amurka.
Farfesa Bensel ya ce, abin da yafi dangane da janyewar sojojin Amurka daga Afghanistan shi ne, yadda suka janye ba tare da sun yi wani shiri na taimaka ma kasar ba domin ta tsaya a kan kafafunta, ta fuskoki na tsaro da tattalin arziki da kuma kyautata rayuwar jama’ar kasar, domin kasantuwar Amurka yasa kasar a cikin manyan kalubale a dukkanin wadannan fuskoki.