Falesdinu; Gwamnatin Isra’ila Ta Mika Kai Ga Bukatun Fursinoni Falesdinawa.
Jami’i mai kula da al-amuran watsa labarai na kungiyar fursinoni falasdinawa ya tabbatar da cewa gwamnatin haramtacciyar kasar Isar’ila HKI ta aminci da dukkan bukatun fursinoni falasdinawa saboda yajin cin abinci wanda dukkan fursinonin falasdinawa suka fara.
Majiyar muryar JMI ta nakalto Kadri Abubakar yana fadar haka ya kuma kara da cewa a cikin makonin da suka gabata fursinoni falasdinawa sun dauki makatai daban daban na kubutar da falasdinawna da suke cikin jidajen yarin yahudawan, wanda suka hada da, rashin amincewa da zuwa kotu, rashin amincewa da tsare falasdinawa saboda matsalolin tsaro, yajin aiki a cikin gidajen yari, da kuma yajin cin abinci.
Labarin ya kara da cewa daga cikin bukatun falasdinawan dai aikwai sauyawa fursinoni wadanda aka yenkewa hukuncin daurin rai dai wuri a duk watannin6.
Tun bayan da falasdinawa 6 suka tsere daga wani gidan yari a Falasdinu a shekara ta 2021 hukumomin gidajen yarin yahudawan suka fara takurawa fursinoni.