Falasdinu; Yara 15 Ne Sojojin Isra’ila Suka Kashe Daga Farkon Wannan Shekarar.
Kungiyar kare hakkin yara wacce aka fi sani da DCI-P wacce kuma take fa cibiya birnin Vienna, ta bada rahoton cewa daga farkon wannan shekara ta 2022 zuwa yanzu sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila (HKI) sun kashe yara falasdinawa har 15 a yankunan su da take mamaye da su.
Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto kungiyar tana fadar haka a wani rahoton da ta fitar a jiya Lahadi, ta kuma kara da cewa sojojin HKI sun kashe yari 5 daga cikin 15 ne a garin Jenin wadanda ke araewacin birnin Qudus a cikin wannan lokacin.
Rahoto ya kara da cewa banda wadanda suka kashe sojojin HKI sun kama yara 17 a cikin wannan lokacin. Sannan wasu akalla 6 kuma suka ji rauni.
A wani bangaren kuma rushe-rushen gidajen Falasdinawa a yankunan su da yahudawan suke mamaye da su ya sanya akalla yara 17 basu da gidan zama a garin Jenin daga yankunansu da aka mamaye.
Rahoton ya kammala da cewa goyon bay aba iya wanda gwamnatin kasar Amurka da kuma na kasashen yamma suke bawa HKI su ne suka bata karfin guiwan ci gaba da aikata abinda suka ga dama a kasar Falasdinu da aka mamaye.